Abinda Muke Yi Domin Kwankwaso Ya Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Diri
- Gwamnan Bayelsa ya bayyana kokarin da suke yi na ganin Kwankwaso ya dawo gidan da aka sanshi watau PDP
- Kwankwaso, mai neman zama shugaban kasa a NNPP ya kai wa Douye Diri ziyara har gidan gwamnati dake Yenagoa
- Diri ya ce jam'iyyar PDP ake wa kallon zata iya kawo karshen matsalolin Najeriya a zahirance
Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya ce shi kansa da wasu ƙusoshin siyasa suna ta Addu'a Allah ya karkato da hankalin Rabiu Kwankwaso ya koma PDP.
Diri ya faɗi haka ne yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Kwankwaso, ya jagoranci tawagar kamfensa suka kai masa ziyara har gidan gwamnati, Yenagoa ranar Talata.
Gwamnan, wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo, ya ce gwamnatinsa na da tunani iri ɗaya da Kwankwaso game da matsalolin da suka addabi ƙasa.
Jaridar Punch tace gwamna Diri, mamban jam'iyyar PDP ya bayyana Kwankwaso da, "cikakken ɗan siyasa," wanda burinsa a yi aiki don gyara goben Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma a cewar Diri abubuwan da suka bayyana a zahirance sun nuna cewa jam'iyyar PDP ce zata iya ceto ƙasar nan daga duhun da aka jefa ta a ciki.
Diri ya kuma kira jihar Bayelsa da ɗaya ɗaga cikin wuraren da ta'addanci ya yi wa illa a duniya ga tsabagen Talauci da ya yi wa jama'a katutu wanda ke bukatar ɗaukin gaggawa.
Wane irin shugaban kasa Bayelsa take so?
A jawabinsa, gwamna Diri ya nuna cewa abinda jihar da mutanenta ke bukata shi ne shugaban kasan da zai tabbatar da adalci kuma wanda zai bi tsarin jamhuriya na ainihi wajen raba arzikin ƙasa.
Sun news ta rahoto gwamnan na cewa:
"Mun amince da kai kan bukatar ceto Najeriya. Da farko ka nuna kana tsammanin mu zo mu haɗe da kai, amma ina son faɗa maka muna ta Addu'ar Allah ya sa ka dawo PDP, gidan da aka sanka."
A wani labarin kuma Dan takarar gwamna a jihar Bauchi a zabe mai zuwa ya hakura, ya koma jam'iyyar PDP
Auwal Isa tare da ɗumbin magoya bayansa a jam'iyyar APM sun ayyana goyon bayansu ga kudirin tazarcen gwamna Muhammed.
Shugabar matan APC ta shiyyar arewa maso gabas da shugabar matan NNPP a Bauchi duk sun bi sahu zuwa PDP.
Asali: Legit.ng