Anyi An Gama: Nayi Kuskuren Marawa Buhari Baya Bazan Sake Irin Wannan Kan Tinubu Ba

Anyi An Gama: Nayi Kuskuren Marawa Buhari Baya Bazan Sake Irin Wannan Kan Tinubu Ba

  • Tinubu da bashi da wata manufa ga yan arewa, kuma akan mai zan zabenshi ko zan mara masa baya
  • An sha mu mun warke duk wanda zamu marawa baya sai yana da manufa da kuma tsarin ci gaban yankin mu
  • Tinubu bazai iya ba shi yasa naki mara masa baya, sabida ina tsoron ai haihuwar guzuma, ya kwance uwa kwance

Abuja - Yayin da zaben shekarar 2023 yake tahowa, tsohuwar jigo a jam'iyyar APC kuma daya daga cikin membobi a hukumar yan sandan Nigeria ta bangarar da tafiyar shugaba buhari ta dau tafiyar Aituku.

Hajiya Naja'atu Muhammad tace baza kuma maimata kuskuren da tai a baya ba, kan marawa Buhari baya tazo ta kuma marawa Tinubu baya kuma.

Naja'atu tace ta bi Buhari ido rufe, ba tare da manufa da kuma wasu kudirorin ci gaba ba, dan haka bazata kuma maimata wannan kuskuren ba.

Kara karanta wannan

2023: Ku zabi mijina, Idan ya gaza laifi na ne, matar Atiku ta roki a hukunta ta

A wata Tattaunawa da tai da gidan talabijin na Trust Tv, a wani shiri mai suna "Daily Politics" tace ta na bin bayan Buhari tun 2002 amma yanzu ya ci amanarta da yan kasa suke tunani daga gareshi.

Naja tace:

"Ni da da wasu miliyoyin da suke son Buhari, sabida sun yarda zai kawo sauyi kan abubuwan da suke faruwa a Nigeria, kuma da yawa-yawan mu bamu taba cewa yai mana wani abu ba, amma duk da haka bai kai mu ga gaci ba, dan haka yanzu zamu sake lale, sabida an sha mu mun warke"

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Naja tace abinda zai fi damunta shine:

Naja'atu
Anyi An Gama: Nayi Kuskuren Marawa Buhari Baya Bazan Sake Irin Wannan Kan Tinubu Ba Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Buhari ya watsawa magiya bayansa ruwa a fuska, basu ba har da mu, maganar da nake maka bamu taba zuwa gidan gwamnati ba, kuma duk wani alkwari da yayi kan cin hanci, tsaro, noma da kuma tabbatar da Nigeria daya bai cika shi ba ya kasa"

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

Gwamnatin Buhari tafi kowacce gwamnati cin hanci da rashawa a Nigeria

naja'atu ta ci gaba da cewa wannan gwamnatin da muke ciki, itace gwamnati mafi muni wajen cin hanci da rashawa, kuna gani fa ya yafewa wasu manyan barayin gwamnati wanda suka debi kudin al'umma masu yawa.

"yanzu mafa maganar da ake ta tiriliyan ce ba biliyan ba fa, kuma bamu ji ya bada wani umarni kan wannan zargin ba, ai dan haka nace ya gaza kuma ya kasa."

Naja'atu tace dan haka bazan kuma yin kuskuren zabar Asiwaju ba, sabida duk kanwar ja ce ba mis

Naja'atu tace sunyi magana da Tinubu kan manufofinsa ga arewa amma yace mata bashi da shi, sai ya ci zai samar. Sannan bai da wata cikakkiyar lafiya da zai iya kamar yadda ta ganshi a London.

Asali: Legit.ng

Online view pixel