Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, Tare Da Mabiyansa Sun Fita Daga APC

Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, Tare Da Mabiyansa Sun Fita Daga APC

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Sanara Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Bindow ya mulki jihar Adamawa tsakanin 2015 da 2019.

Ya aike wasikar fita daga APC ga shugaban jam'iyyar na gundumarsa ta Kolere, karamar hukumar Mubi ta Arewa ranar 20 ga Junairu, 2023, rahoton Leadership.

Dan siyasan dai har yanzu bai bayyana inda ya dosa ba amma ya ce dubunnan masoyansa zasu yi hijira da shi domin hada kan al'ummar Adamawa.

Bindow
Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, Tare Da Mabiyansa Sun Fita Daga APC Hoto: Leadership
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, ya fita daga APC ne saboda rashin sulhun gaske tsakanin 'yayan jam'iyyar tun bayan shan kashin da yayi a zaben 2019 da kuma rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwanin 2022.

A cewar wasikar:

"Ina mai sanar da kai cewa nayi murabus matsayin mamban jam'iyyar All Progressive Congress party (APC) daga ranar 20 ga Junairu, 2023."
"Na yanke wannan shawara ne bayan addu'o'i da shawara da iyalaina, masu ruwa da tsaki da kuma mabiya a fadin jihar da kasa gaba daya."
"Na yi hakan ne bisa rashin jituwa da sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ta Adamawa tun bayan abinda ya faru a zaben 2019 da kuma bayan zaben 2022."
"Hakazalika ina sanar da kai cewa mabiyana na biye da ni wajen fita daga jam'iyyar don shiga sabuwar harkar hada kan al'ummar Adamawa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel