Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Buhari

Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Buhari

  • Jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom ta ɗauki mataki kan tsohon mai ba Buhari shawara, Sanata Ita Enang
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Kotun ɗaukaka kara ta bayyana sahihin dan takarar gwamnan APC
  • Shugaban APC a jihar ya tabbatar da lamarin inda ake zargin Enang da yi wa PDP aiki ta bayan fage

Abuja - Kwanaki kaɗan bayan Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta ayyana Akanimo Udofia a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan APC a Akwa Ibom, wata sabuwar rigima ta kunno kai.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wata wasiƙa da ta bayyana a Intanet ta nuna cewa APC ta kori Mista Ita Enang daga inuwar jam'iyyar bayan rashin nasarar da ya yi Kotu.

Sanata Ita Enang.
Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Buhari Hoto: premiumtimes
Asali: Facebook

Mista Enang, tsohon mashawarci ne ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma ya nuna bai yarda da sakamakon zaben fidda gwanin gwamna ba a Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

2023: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Shigar da Gwamnan Arewa

Wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban APC na jihar Akwa Ibom, Stephen Ntukekpo, da kwanan watan 24 ga watan Janairu, 2023 kuma an aikata ga shugaban APC na gundumar Mista Enang.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta shaida wa shugaban jam'iyya na gundumar da ke karamar hukumar Iɓiono Ibom a Akwa Ibom cewa APC ta kori Enang ne saboda shigar da ƙarar da ya yi kan tikitin takarar gwamna.

Legit.ng Hausa ta gano cewa Enang, tsohon Sanata ya zarce zuwa Kotun Koli domin kalubalantar hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara kan sahihin dan takarar gwamnan APC a Akwa Ibom.

Jam'iyyar APC ta zargi Mista Enang da yi wa jam'iyyar PDP aiki ta karkashin ƙasa yana cin amanarta

A wasikar, Mista Ntukekpo, yace kwamitin gudanarwa na APC reshen jihar ya ɗauki wannan matakin ne kan korafin da aka kai masa game da halayen tsohon hadimin Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Shugaban APC na jihar, ranar Talata, ya tabbatarwa jaridar cewa wasikar dake yawo ta korar ɗan siyasan ta gaskiya ce. Sai dai Enang yace bai da masanuya kan korar, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

A nasa bangaren, ɗan takarar gwamnan APC a Akwa Ibom, Musta Udofia, da aka nemi jin ta bakinsa kan ci gaban, ya ce:

"Ban san meyasa kuka mun wannan tambaya ba, harkoki ne na jam'iyya, ina ga shugabanni APC ne suka fi da cewa su ba da wannan amsa."

Kotu ta jika wa APC aiki a jihar Benuwai

A wani labarin kuma Kotu Ta Umarci a Sauya Zaben Fidda Gwanin APC a Kananan Hukumomi 11 Na Benue

A cewar Kotun, ta yanke wannan hukuncin ne bayan gamsuwa da bayanan masu ƙara da kuma waɗanda ake kara game da zaben fidda ɗan takarar gwamna.

Alkalin Kotun yace APC ta gudanar da zaben a kananan hukumomi 12 cikin 23 na jihar Benuwai, ta koma ta shirya a sauran kafin fitar da sakamakon ƙarshe.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262