Sanata Ahmad Lawan Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu a Taron Bauchi
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya tabbatar da goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu
- Yayin da yake jawabi a wurin ralin APC a jihar Bauchi, Sanata Lawan ya yaba wa Buhari bisa nasarorin da ya samu a arewa maso gabas
- Sanatan yace ya dace arewa maso gabas ta zabi Tinubu da APC domin nuna godiya ga abinda shugaba Buhari ga musu
Bauchi - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roki mutanen arewa maso gabashin Najeriya su jefa wa Bola Ahmed Tinubu kuri'unsu a zabe mai zuwa.
Lawan ya faɗi haka ne a wurin Ralin kamfen APC da ya gudana a Bauchi ranar Litinin 23 ga watan Janairu, 2023 wanda ya samu halartar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Sanata Lawan ya yi wannan roko ne a wata sanarwa da Abdulaziz Abdulaziz, mambam sashin midiyan Tinubu ya aike wa Legit.ng Hausa.
Shugaban Sanatoci ya yabawa Buhari
Da yake jawabi a wurin Ralin, Sanata Ahmad Lawan ya jinjina tare da yabon shugaban ƙasa Buhari, inda yace ya sauke nauyin da aka dora masa kana ya sa jam'iyya mai mulki alfahari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace tururuwar da mutane suka yi suka hallara a wurin gangamin wata alama ce dake nuna arewa maso gaban na godiya da kokarin Buhari na ceto su daga bala'in Boko Haram.
A kalamansa, Lawan ya ce:
"Jam'iyyar PDP ta bar arewa maso gabas hannun Boko Haram, sun barmu a hannun 'yan ta'adda su kashe mu, ta kai ga idan muka yi korafi sai a ɗora mana laifin, amma daga zuwanka ka sauya zancen."
"Ya rataya a wuyan mu a yanzu mu ci gaba da yin abinda ake tsammani ta hanyar zaben APC domin sakawa amfanar da muka yi da shugabancinka."
Kotun Daukaka Kara Ta Kori Ɗan Takarar Gwamnan APC
A wani labarin kuma Kotun daukaka kara ta tsige dan takarar gwamnan APC a jihar Benuwai, ta ce zaben fidda gwani bai kammalu ba
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Makurdi, jihar Benuwai, ta umarci sake shirya zaben fidda ɗan takarar gwamnan APC a kananan hukumomi 11 na jihar.
Kotun ta baiwa APC mako biyu a shirya zaben kuma tace har sai an kammala ne za'a bayyana wanda ya yi nasarar zama ɗan takarar gwamna.
Asali: Legit.ng