Jam'iyyar PDP Ta Nemi NDLEA, EFCC Su Damke Bola Tinubu Na APC
- Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya yi kira da EFCC, NDLEA su kama Bola Tinubu su titsiye shi
- Bwala, mai magana da yawun PCC-PDP yace ɗan takarar shugaban kasan yana da tambayoyin da ya kamata ya amsa
- A yan makonnin nan dai ana ta cece-kuce tsakanin manyan yan takarar shugaban kasa biyu watau Tinubu da Atiku
Abuja - Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga mahukunta su gaggauta cafke Bola Ahmed Tinubu, mai neman shugaban kasa na APC.
PCC-PDP ya bukaci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) su damƙe Tinubu ya amsa tambayoyi.
Kwamitin kamfen Atiku/Okowa ya yi wannan kira ne a wurin taron manema labarai dake gudana yanzu haka a Abuja, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Mai magana da yawun kwamitin PCC-PDP na kasa, Daniel Bwala, ya ce ya zama wajibi NDLEA ta tsoma baki, ta kira Tinubu ya mata karin haske kan badakalar da ta sanya ya biya Amurka dala $460,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan haka Bwala ya yi Allah wadai da wata tawaga da ake zargin Tinubu ne ya haɗa ta ana ce mata "Mayaka."
Kakakin PCC-PDP ya yi kira da hukumomin tsaro da su cafke tare da gurfanar da duk wanda ke da alaƙa da tawagar da suke wa laƙabi da, 'Sojojin Jagaban'.
Ya ƙara da cewa mambobin tsagin adawa da dama sun ci karo da sakon barazana yayin da ake tunkarar babban zabe.
Tinubu na da hannu a safarar kwayoyi - PDP
Da yake kara karfafa Bwala, wani kakakin kamfen PDP, Phrank Shaibu, ya yi ikirarin cewa har yau Tinubu na taɓa kasuwancin kwayoyi tun daga shekarar 2015.
Ya ce tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya tura maƙudan kuɗi dala miliyan $4.3m zuwa wani Kamfanin kwantena da ke a ƙasar Colombia, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A wani labarin kuma Gwamna Yahaya Bello Ya Musanta Rahoton Ya Janye Daga Goyon Bayan Tinubu a Zaben 2023
Gwamnan jihar Kogi kuma Koodinetan matasa na PCC-APC, Yahaya Bello, ya musanta rahoton da ke cewa ya tsame kansa daga jirgin yakin zaben Tinubu.
Gwamna Bello yace goyon bayan da yake wa Tinubu da abokin takararsa Sanata Kashim Shettima bai canza ba.
Asali: Legit.ng