Zargin Cin Hanci Da Rashawar Atiku: Jam'iyyar PDP Ta Maidawa APC Martani

Zargin Cin Hanci Da Rashawar Atiku: Jam'iyyar PDP Ta Maidawa APC Martani

  • Kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar PDP, hadi mai magana da yawun jam'iyyar sun maida martani kan zargin dan takarar su da suka ce anyi
  • Jam'iyyar APC, ta hannun masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar sun bukaci da EFCC da ICPC da su damke Atiku a cikin kwana uku
  • Sun rubuta bukatarne dan neman tuhumar Atikun da zargin karkatar da dukiyar gwamnati ba bisa ka'ida ba

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar PDP, ya nemi da jam'iyyar APC mai mulki ta bata hakuri kan zargin cin hanci da rashawa da tayiwa dan takararta, Alhaji Atiku Abubakar

Kwamitin kuma ya zargi dan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da barnatar da dukiyar jam'ar jihar Lagosn daga shekarun 1999 zuwa 2007. Rahoton Premium Times

Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ya fitar da wata takardar a ranar litinin inda yake neman hukumar EFCC da ICPC da su cika hannu da dantakarar jam'iyyar PDP sabida zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Jama'ar Kano ne suka ce na fito takara, ba yin kaina bane: Inji Dan Takarar Gwamnan Kano

Atiku/Tinubu
Zargin Cin Hanci Da Rashawa Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Tace Dan Takarar Ta Bai Sace Kudin Jama'ar Lagos Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Keyamo wanda ya ke zantawa da yan jaridu yayin sakin takardar, ya ce kamata yai Atiku ya dakatar da yakin neman zabe ya fuskanci zargin da ake masa

Yayin da shi kuma mai magana da yawun jam'iyyar PDP ke maida martani kan wannan batu Kola Ologbodiyan, yace:

"Wannan zargin sai dai Tinubu amma ba Atiku ba, sabida shi aka zarga da karkatar da dukiyar jama'ar jihar Lagos.

Jam'iyyar PDP ta nemi da jam'iyyar APC ta bata hakuri kan wannan bata suna da tai mata na zargin cin hanci da rashawa ga dan takarar ta Atiku Abubakar, kamar yadda jaridar Headlines ta rawaito

Tinubu ne ya barnatar da dukiyar jihar lagos daga 1999 zuwa 2007

Tinubu na tunanin akwai laifuka da yawa akansa na cin hanci, musamman ma lokacin da yake gwamnan jihar Lagos, to shi ne yake so ya maida zargin kan dan takarar mu sabida yaga ya fishi farin jini, inji mai magana da yawun jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

"Dan haka muke kalubalantar jam'iyyar APC kan ta fitar da wani kundi ko bayani daga bankunan kasuwanci na kasa da aka ga alama ko kuma tabbacin wulgawar wasu kudade da basu kamata ba da sunan atiku."
"Muna kalubalantar dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu da yai bayanin yadda jihar Lagos ke karbar Haraji na musamman daga wasu kamfanunuwa wanda mallakin Tinubun ne."

Sannan muna kalubalantarsa da yai bayanin yadda aka sai motocin miliyan dari wanda aka ce na musamman ne, dan amfanin ofis da kuma wasu hidn-dimu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel