Zaben 2023: Zan Warware Wasu Tsare-Tsaren El-Rufa'i Idan An Zabe Ni Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Zaben 2023: Zan Warware Wasu Tsare-Tsaren El-Rufa'i Idan An Zabe Ni Gwamnan Kaduna, Uba Sani

  • Sanata Uba Sani dan takarar gwamnan Jihar Kaduna karkashin APC ya ce zai warware wasu tsare-tsaren gwamna Nasir El-Rufai idan ya ci zabe a 2023
  • Sani ya ce El-Rufai mutum ne don haka dole ne a iya samunsa da aikata kura-kurai kuma zai sauya duk wani tsari da al'ummar jihar suka nuna damuwa a kansa
  • Takwarorinsa na jam'iyyar PDP, Isa Ashiru da Suleiman Hunkunyi na NNPP sun sha alwashin rushe tsare-tsaren APC da mutane ka korafi kai idan sun samu mulki a 2023

Kaduna - Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce ya yi alkawarin sake duba wasu tsare-tsaren gwamnati mai ci yanzu da mutane ke ganin ba su musu dadi ba.

Da ya ke magana yayin muhawara da BBC Hausa ta shiryawa yan takara a Kaduna, a ranar Laraba, Sani ya ce El-Rufai dan adam ne don haka yana iya yin kuskure.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutum 25 Sun Mutu A Yayin Da Sabuwar Mugunyar Cuta Ta Ɓulla A Kano

Uba Sani da El-Rufai
Zaben 2023: Zan Warware Wasu Tsare-Tsaren El-Rufa'i Idan An Zabe Ni Gwamnan Kaduna, Uba Sani. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya amsa cewa ta yiwu a samu kura-kurai a tsare-tsaren El-Rufai a bangarorin ilimi da cigaban al'umma, Daily Trust ta rahoto.

Amma, ya bayyana karara cewa zai cigaba da ayyukan alheri da gwamnatin El-Rufai ta fara.

Ya ce:

"Zan duba wasu tsare-tsare kuma in gyara wadanda akwai kura-kurai. Saboda shi gwamnan dan adam ne, dole ya yi wasu kura-kurai kuma za a gyara wadannan. Zan cigaba da tsare-tsaren masu kyau."

Ashiru Da Hunkuyi sun soki wasu tsare-tsaren gwamnatin El-Rufai

A wani jawabi daban, dan takarar jam'iyyar New Nigerian Peoples Party candidate, Senator Suleiman Hunkuyi, da takwararsa na PDP, Isa Ashiru, duk sun sha alwashin warware tsare-tsaren gwamnatin jihar Kaduna kan ilimi da korar malamai da karin kudin jami'ar Kaduna.

Yan takarar biyu sun yi ikirarin cewa yara da dama sun dena zuwa makaranta saboda karin kudin da gwamnan ya yi.

Kara karanta wannan

NDLEA Tayi Abin da Ba a Taba Yi ba a Tsawon Shekara 33 a Karkashin Buba Marwa

Ashiru ya yi ikirarin cewa mafi yawancin makarantun gwamnati a jihar ba su da kujeru da tebura duk da cigaba da gwamnatin ta ce ta kawo a bangaren ilimi.

A cewarsa, za a kafa kwamiti da za ta duba batun korar malamai da ma'aikatan gwamnati da gwamnatin APC ya yi, yana mai cewa za a dawo da wadanda aka kora bisa kuskure.

Hakazalika, dan takarar NNPP, Sanata Hunkuyi shima ya yi alkawarin warware batun korar malaman makaranta tare da taimakon wadanda gwamnatin APC ta rushe musu shaguna.

Takaitaccen tarihin Sanata Uba Sani

A baya, Legit.ng ta tattaro muku bayanai kan takairaccen tarihin sanatan na Kaduna ta tsakiya da gwamna El-Rufai ke fatan zai gaje shi.

Sani haifafan garin Zaria ne kuma an haife shi a shekarar 1970 kamar yadda bayanai daga Wikipedia ta nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164