An Ji Labarin Abin da Tinubu Ya Fadawa ‘Yan Takaran APC a Kan Takara da Lafiyarsa
- Asiwaju Bola Tinubu ya yi zama na musamman da duka masu neman kujerun siyasa a jam’iyyar APC
- Bola Tinubu ya fadawa abokan tafiyarsa cewa ya zama dole su ci zabe domin gudun APC ta ji kunya
- Tinubu ya ce yana ratsa lungu da sako wajen kamfe, hakan martani ne ga masu cewa bai da koshin lafiya
Abuja - A matsayinsa na ‘dan takaran shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya zauna da sauran masu neman mulki a jam’iyyar APC a zaben bana.
A ranar Lahadi, 15 ga watan Junairu 2023, Premium Times ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya hadu da masu neman kujerun siyasa a jam’iyya mai mulki.
Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan takaran da su hada-kai wajen yi wa APC aiki a babban zabe, yake fada masu cewa dukkansu na da bukatar kowanensu.
An rahoto ‘Dan takaran kujerar shugaban kasar yana cewa aiki ne a gabansu na ganin sun kai jam’iyyar APC ga nasara domin su kai kasar ga ci.
Dole mu lashe zabe - Tinubu
A cewar tsohon Gwamnan na jihar Legas, yana da matukar muhimmanci ga jam’iyyar APC ta lashe zabe ma zuwa, idan ana son cigaban kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta rahoto Bola Tinubu yana bayanin yadda ya kagara ya gana da ‘yan takaran jam’iyyarsu, ya yi kira a gare su da ka da su bada kunya.
A ra’ayin Tinubu, ganin yadda gwamnatin PDP ta jagoranci Najeriya a lalace na tsawon shekaru, burin mutanen Najeriya yana kan ‘yan takaran APC.
Vanguard ta ce Tinubu ya fadawa masu neman takarar cewa an kafa APC ne ba da nufin ta zama jam’iyyarsa kurum ba, sai saboda ta ceci jama’a daga PDP.
Tun da jam’iyya ta ba su damar samun tikiti, ‘dan takaran shugaban kasar ya fadawa wadanda suka halarci taron cewa dole su dage a babban zabe da ke zuwa.
Bola Tinubu bai da lafiya?
Tinubu ya ce yana ta zagaye ko ina, abin da ‘yan adawarsa sun gagara yi, alkawarin da ya yi shi ne zai tafi da kowa idan ya zama shugaban Najeriya.
'Dan takaran yana ganin zaben ba ta shi ba ne kawai, aiki ne a gaban duka jam'iyya.
“Ku na bukutata kamar yadda nake bukatarku.
Idan na yi maku aiki, kai na nake taimako; idan ku ka jawo mani jama’a, kanku ku ke taimako a lokaci daya. Makomarmu duk a tare suke.
- Bola Tinubu
Emi Lokan
A rahoton da muka fitar, an ji Fasto Tunde Bakare ya ja-kunnen Jama’a a kan zaben ‘dan siyasar da ke cewa yanzu lokaci yayi da zai karbi ragamar mulki.
Faston ya ce mutanen Najeriya suyi hattara da ‘dan takaran da bai zuwa wajen muhawara, kuma ya gagara bayani ga jama’an da yake neman kuri’unsu.
Asali: Legit.ng