Zaben 2023: Dubban Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Bauchi

Zaben 2023: Dubban Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Bauchi

  • Jam'iyyar APC a jihar Bauchi ta yi gagarumin rashi na dubbannin mambobinta gabannin babban zaben 2023
  • Mambobin jam’iyya mai mulki a kasar fiye da 20,000 sun sauya sheka zuwa PDP a kananan hukumomi 20
  • Masu sauya shekar sun ce sun koma jam'iyyar Gwamna Bala Mohammed ne saboda tarin nasarorin da ya samu a jihar

Bauchi - Akalla mambobin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) 20,350 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jahar Bauchi.

Jaridar PM News ta rahoto cewa mai ba Gwamna Bala Mohammed shawara ta musamman kan harkokin siyasa ne ya bayyana hakan yayin da yake tarbar masu sauya shekar a wani taro da aka gudanar a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu a garin Bauchi.

Taron kona tsintsiya
Zaben 2023: Dubban Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Bauchi Hoto: PM News
Asali: UGC

A cewarsa, masu sauya shekar sun fito ne daga fadin kananan hukumomi 20 da ke jihar.

Kara karanta wannan

Makonni Gabanin Babban Zabe, Babban Jigon APC Kuma Tsohon Kwamishina Ya Bar Tsagin Tinubu

Dalilinmu na barin APC zuwa PDP - Masu sauya sheka

Daya daga cikin masu sauya shekar, Bala Zungur ya ce sun sauya sheka ne daboda gagarumin nasara da jam'iyyar PDP mai mulki ta samu musamman ma a bangaren ci gaban ababen more rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zyungur ya ce gwamnatin Bala Mohammed ta gina hanyoyi mai tsawon dubban kilomita a birni da kakkara, ta gina makarantu, asibitoci da sauran muhimman ayyuka don inganta rayuwar mutane a jihar.

Ya ce masu sauya shekar sun hada da masu ruwa da tsaki na APC da shugabannin jam'iyyar a fadin gudunmar zabe, yana mai cewa za su marawa PDP baya don bata damar ci gaba da samun nasara a jihar.

Zungur ya bukaci shugabannin PDP a matakan jiha da kasa da su karbe su cikin jam'iyyar bisa adalci, da daidaito sannan ya yi alkawarin goyon bayan yan takararta a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar NNPP Ta Yi Kasa-Kasa da PDP, Ta Zama Babbar Jam'iyar Adawa a Majalisar Jihar Arewa

Ya ce:

"Mun bar APC saboda ta gaza magance rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta wanda ka iya sa ta shan kaye a babban zaben 2023.
"Masu sauya shekar a nan wajen sun yi aiki sannan sun marawa APC baya tsawon shekaru takwas, amma jam'iyyar tana tafiya babu alkibla, mun yanke shawarar komawa PDP don ciyar da jahar gaba.
"Mutane 1,000 a fadin kananan hukumomi 20 sun sauya sheka zuwa PDP, kuma dukkaninsu suna nan tare da mu."

A halin da ake ciki, Zungur ya bukaci gwmnan da shugabancin jam'iyyar da su kare ra'ayin masu sauya shekar, rahoton The Guardian.

Atiku ya yi tuntuben harshe a Kogi, ya ce a zabi APC

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Kogi, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi subul da baka inda ya nemi a zabi jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng