2023: Atiku Ya Yi Subul Da Baki A Kogi, Ya Ce A Zabi AP...PDP A Zaben Shugaban Kasa, APC Ta Sakin Bidiyon

2023: Atiku Ya Yi Subul Da Baki A Kogi, Ya Ce A Zabi AP...PDP A Zaben Shugaban Kasa, APC Ta Sakin Bidiyon

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 25 ga watan Fabrairu, ya yi subul da baka a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu
  • Yayin kamfen dinsa na shugaban kasa a jihar ta arewa, Atiku ya bukaci magoya bayansa da suka taru da su zabi APC
  • Amma, cikin gaggawa tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa kansa gyara ya ce mutane su zabi PDP
  • Da ta ke martani kan lamarin, APC ta ce wannan ba shine karo na farko da Atiku ke yin irin wannan kuskuren ba yayin kamfen

Kogi - Yayin kamfen din shugaban kasa a Kogi, Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, cikin kuskure ya bukaci mutane su zabi jam'iyyar APC.

Amma, Atiku ya gane kuskurensa kuma cikin gaggawa ya gyara ya fada wa mazauna jihar su goyi bayan jam'iyyar PDP a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito

Atiku a Kogi
2023: Atiku Ya Yi Subul Da Baki A Kogi, Ya Ce A Zabi AP...PDP A Zaben Shugaban Kasa, APC Ta Saki Bidiyon. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke martani kan hakan, kakakin kwamitin kamfen din jam'iyyar APC, Festus Keyamo ya ce idan da Asiwaju Bola Tinubu ne ya yi wannan, da labarin ya bazu a kafafen watsa labarai.

Keyamo, a cikin sakon da ya wallafa a Twitter, a ranar 14 ga watan Janairu, ya kara da cewa wannan ba shine karon farko da Atiku ke yin irin wannan kuskuren ba yayin kamfen.

Kalamansa:

"Yanzu Atiku Abubakar a Kogi ya ce yan jihar su zabi jam'iyyar APC, sai nan take ya gyara kuskuren da ya yi.
"Yanzu, idan ta ace @OfficialABAT ne da kafafen watsa labarai sun fara ihun 'subul da baka'. A lura, ba wannan ne karo na farko da Atiku ya ke yin irin wannan kuskuren ba yayin kamfen."

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shugaban Kasa Mai Jiran Gado a 2023

Da ya ke magana a yayin kamfen din a jihar, Atiku ta shafinsa na Twitter ya ce:

"Yau, Kogi ta sake jadada sunanta na wurin haduwa ta yadda mutane masu yawa suka hadu a Confluence Stadium. Dama ce mai kyau a fada wa mutanen Kogi abin da jihar za ta iya samarwa.
"Na fada musu cikin tsarin fafardo da kasa na @OfficialPDPNig akwai gina tashar kan tudu na Kogi, wanda zai amfani jihohin arewa, tare da kawo karshen rike wa ma'aikata albashi a jihar."

2023: Dino Melaye ya yi wa Tinubu ba'a kan subul da baka a wurin kamfen

Sanata Dino Melaye, kakakin kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, ya yi wa Bola Tinubu na APC ba'a kan yin subul da baka yayin kamfen a Legas.

Jigon na jam'iyyar PDP ya ce yana tausaya wa Tinubu ya kuma yi masa addu'a Allah ya bashi lafiya.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164