Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock
NESG ta na zama da ‘yan takaran shugaban kasa domin jin manufofinsa a bangaren tattalin arziki
Asiwaju Bola Tinubu ya nuna zai dauko kwararru, ya yi aiki da ‘yan kasuwa idan ya iya karbar mulki
Gwamnatin Tinubu za ta janye tallafin man fetur, kuma da alama ba za ta ji tsoron cin bashi ba
Lagos - Asiwaju Bola Tinubu mai neman mulkin Najeriya a jam’iyyar APC ya gabatar da manufofin da yake da shi wajen ganin ya gyara tattalin arziki.
Da yake jawabi a wajen taron NESG ranar Juma’a a garin Legas,The Cable ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya yi bayanin manufofin da yake tattare da su.
‘Dan takaran shugaban kasar ya ba gwamnatin Muhammadu Buhari kariya, yana mai cewa gibin da ake da shi a kasafin kudin Najeriya ba matsala ba ce.
A cewar tsohon Gwamnan na Legas, kasashen da suka fi kowane cigaba a Duniya, suna tattare da bashi, yake cewa cin bashin salo ne mulki a zamanin yau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tinubu ya sha bam-bam da masana
A wajen zaman da NESG tayi da masu neman takarar shugabancin Najeriya, Bola Tinubu ya ce bai yarda da hanyar da ake bi wajen magance tsadar kaya ba.
An rahoto ‘dan takaran yana cewa bai ganin farashi za su sauka saboda bankuna sun kara ruwa watau riba a kan bashi ko kuma an tsuke tattalin arzikin kasa.
Har ila yau, ‘dan siyasar yana ganin ta kasafin kudi ne za a fi a gyara tattalin arziki cikin sauki ba da tsarin kudi da babban bankin Najeriya yake kula da shi ba.
Tallafin man fetur
Kamar yadda Vanguard ta kawo rahoto, a wajen ne Tinubu ya sake jaddada cewa babu dalilin gwamnatin tarayya ta cigaba da kashe kudi a kan tallafin fetur.
Gwamnatin Tinubu za ta cire tallafin man fetur kaco-kam, domin a ganinsa ana ficewa da man Najeriya ne domin a rika saida su kasashen makwabta da tsada.
Tinubu ya ce ba zai ‘adana’ kudin ba, za a batar da su ne a wajen gina abubuwan more rayuwa na gidaje, asibitoci da makarantu da kuma taimakon marasa hali.
Bola Tinubu zai zabo kwararru da suka san aiki, ya ba su mukamai a kwanaki darinsa na farko. The Nation ta rahoto shi ya ce da ‘yan kasuwa zai yi tafiya.
Ana harin kuri'in Kano
An ji labari cewa Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun kwallafa rai a kan miliyoyin kuri’un da za su fito a Jihar Kano a zaben bana.
Manyan ‘Yan takaran kujerar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyun APC, PDP, NNPP da LP sun fito da dabarun da za su cece su kan sauran abokan gaba.
Asali: Legit.ng