Wike: Idan Muka Rufe Kofa, Ko Sama da Kasa Zata Haɗe Ba Zamu Sasanta da PDP Ba
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce har yanzu jam'iyyar PDP na da damar neman sulhu da tawagar G-5
- Babbar jam'iyar adawa a kasar nan ta rasa zaman lafiya a cikin gida tun bayan gama zaben fidda gwani
- Wike yace idan G5 ta yanke wanda zata marawa baya ko sama da kasa zasu hade ba wanda ya isa ya hana su
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin G-5 zasu kulle duk wata damar tattaunawar neman sulhu a jam'iyyar PDP.
Tun bayan kammala zaben fidda gwanin dan takarar shugaban, babbar jam'iyar hamayya ta rasa zaman lafiya a cikin kan kiraye-kirayen Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga shugaban jam'iyya.
Kiran wanda Gwamna Wike da yan tawagarsa ke jan gaba, sun ce ba zai yuwu dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyya na kasa su fito daga yanki ɗaya ba.
Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023
A wata hira da BBC ranar Jumu'a, gwamna Wike yace ba gudu ba ja da baya matukar aka kai matakin da G-5 ta bayyana dan takarar shugaban ƙasan da zata marawa baya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya ce:
"Abinda nake son faɗa maku shi ne ya kamata PDP ta yi amfani da damarta saboda akwai lokacin da zamu rufe kofa kuma ba abinda zai faru, idan lokacin ya yi ko sama zata faɗo sai dai ta fado."
"Ba wanda zai wa ɗayanmu barazana, idan muka yanke hukunci ba zamu goyi bayan dan takarar PDP ba muna da hujja zamu bayyana dalilanmu kuma wanda zai iya wani abu, ya kamata su kula."
Mu yan siyasa ne muna da dabaru - Wike
A watan Disamba, gwamna Wike yace zai fara tallata dan takarar da ya zaɓa a watan Janairu, amma da aka tambaye shi kan kalamansa a hirar, yace an kammala duk wasu shirye-shirye.
The Cable ta rahoto Wike na cewa:
"Meyasa kuke gaggawa ne? Ban fadi rana ba a watan Janairu, kowa ya kwantar da hankalinsa. Mu yan siyasa ne kuma muna da dabarunmu na siyasa, bani kadai nake aiki ba."
Zamu kafa gwamnatin Musulunci a Katsina - NNPP
A wani labarin kuma 'Dan Takarar Gwamna a 2023 Ya Yi Alƙawarin Kafa Gwamnati Bisa Koyi da Annabi Muhammad SAW
Dan takarar gwamna Katsina na NNPP mai kayan dadi yace zai kafa gwamnatin Musulunci bisa koyarwar Annabi Muhammad SAW idan aka zabe shi.
A wurin taron al'umma da aka shirya wa yan takarar yau Asabar, yace duk ciwon da Najeriya ke fama da su a yanzu haka Musulunci na da maganinsu.
Asali: Legit.ng