Lai Muhammad: Wanda Suke Sukan Buhari Basu San Irin Cigaban Da Ya Kawo Ba

Lai Muhammad: Wanda Suke Sukan Buhari Basu San Irin Cigaban Da Ya Kawo Ba

  • Ba gwamnatin da za'a ce ta aiki dari bisa dari kokuma talakawanta na sonta dari bisa dari, dole ne a samu masu sukanta
  • Wani ministan Buhari yace wanda suke sukar buhari basu san aiyukan da yayi bane shi yasa suke sukarsa
  • Jam'iyyub adawa, mutane da kungiyiyo na sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kan abubuwa da dama ciki kuwa harda cin hanci da rashawa

Abuja - Ministan ma'aikatar labarai da al'adu a Lai Muhammad ya nuna rashin amincewarsa kan batun shugaba muhammadu buhari bai kawo aikin ci gaba ba a Nigeria sai dai koma baya yace wanda suka fadi hakan basuyi adalci ba.

Lai Muhammad
Lai Muhammad: Wanda Suke Sukan Buhari Basu San Irin Cigaban Da Ya Kawo Ba Hoto: This Day
Asali: UGC

Ya fadi hakan ne lokacin da ake auna mizanin yadda shugaba Buhari yayi mulkinsa a karo na sha takwas, kamar yadda jaridar Thisday ta rawaito.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Adawa ko fadin maganganu akan gwamnatin nan basu da muhalli domin shugaba Buhari yayi aikin abin azo a gani, da dukkan wata girmamawa na ke cewa duk wanda yayi wannan batun baida masaniya kan gwamnatin mu"
"Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin shugaba Buhari tayi duk wani abu da za'ace dimukuradiyya ne, kwannan nan ma ga aikin Second Niger Bridge da za'a bude"

Jaridar Daily trust kuma ta rawaito cewa ministan na cewa:

"Kunsa sane da da yadda gwamnatin nan tai aiyukan raya kasa wanda baki bazai iya fadarsu ba, banda kuma yadda ta bunkasa tattalin arziki, rashin adalci ne ace wani yace gwamnatin nan batai komai ba"

Mai Buhari yake yi ake sukarsa

Wanda suke sukar Buhari basu san wadannan abubuwan sune muhimmai wajen raya al'umma ba, yana mai cewa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

"Wannan aiyukan raya kasar sune abubuwan da suke kawo ci gaban tattalin arziki, to kunga cewa muna bunkasa tattalin arzikinmu kenan.

Ministan yace yayi da kake gina tituna da gadoji, to kana samar da aiyukan yi ne sabida za'a dau ma'aikatan da zasu yi aiki, kuma hakan zai bunkasa tattalin arziki

Yawan yin wadannan aiyukan na kawo ci gaba da ba'a taba tunanin yankin da suke zasu same shi ba, inji kinistan.

Ministan yace shugaba Buhari ya samar da da aiyukan tituna a jihohin Nigeria sosai, sannan kuma ya gina sabbin gurabe da cibiyoyin gwamnati a jihohin dai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel