2023: Bani Gishiri In Baka Manda Za Mu Yi Da Inyamurai a Zabe Mai Zuwa, Inji Tinubu

2023: Bani Gishiri In Baka Manda Za Mu Yi Da Inyamurai a Zabe Mai Zuwa, Inji Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya ce bani gishiri in baka manda za su yi da inyamurai a zaben 2023
  • Tinubu ya ce sai Inyamurai sun ba shi kurinsu sannan zai yi masu aiki a matsayin shugaban kasa domin a cewarsa sai an zuba ake kwashewa
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce duk wani yunkuri na hana kudirinsa na son mulkar Najeriya ba zai cimma nasara ba

Enugu - Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya fada ma Inyamurai a Enugu cewa idan suka zabe shi, zai bari su dandani zuma a kasar.

Tinubu ya bukaci al'ummar jahar Enugu da Inyamurai gaba daya da su zabe shi domin su sha romon dadi a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Kwankwaso da Obi za su tashi a tutar babu, malami ya hango magajin Buhari

Bola Tinubu
2023: Bani Gishiri In Baka Manda Za Mu Yi Da Inyamurai a Zabe Mai Zuwa, Inji Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Premium Times ta nakalto Tinubu yana cewa:

"Idan ka zuba jari ne kawai za ka iya girbewa. Idan ku ka zabe ni za ku sha romon dadi a kasar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zan kara daga martabar jahar Enugu idan na gaji Buhari, Tinubu

Da yake magana a Enugu, tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce zai daukaka darajar jihar ta zama cibiyar masana'antu fiye da yadda take a yanzu.

Ya bayyana kungiyar yakin neman zabensa a matsayin jirgin kasa mai tafiya wanda ya shirya lashe zabe, cewa duk wani yunkuri na tsayawa a gaban jirgin kasa da ke kan tafiya zai kare ne a cikin tashin hankali.

Ya ci gaba da cewa:

"Ba za ku iya shiga gaban nasara ba. Rashin sani ne kawai zai sa ka yi yunkurin tsayawa a gaban nasara. Ba ma neman kaso 25 na kuri'u. Muna aiki ba ji ba gani har sai Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya."

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

Dan takarar gwamnan APC a Enugu, Uche Nnaji da Gwamna Hope Uzodinma da Gwamna Umahi ma sun yi jawabi a gangamin, rahoton Peoples Gazatte.

Sai dai sun sha banban kan yawan kari'un da Tinubu zai samu a yankin kudu maso gabas.

Yayin da Nnaji ya ce za su samu kaso 30 cikin dari, Mista Uzodinma ya ce yana sa ran za a kusa yin kan doki, yayin da Umahi ya ce kaso 90 za su samu daga yankin.

Umahi ya ce:

"Ya zama dole mu zabi APC don kada mu sha kaye. Ba ma neman kaso 60 ko kaso 80, illa kaso 100 na kuri'un."

Ka da ku mika Najeriya ga mutumin da bai da lafiya a 2023, Peter Obi

A wani labarin, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya yi kira ga yan Najeriya a kan kada su kuskura su mika kasar ga mutumin da bai da lafiya domin ya mulke su.

Obi ya bayyana cewa kasar na cikin wani hali a yanzu kuma mika ta ga mara lafiya zai kara kawo matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel