2023: Watanni Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Mutu, PRP Ta Maye Gurbinsa a Ogun

2023: Watanni Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Mutu, PRP Ta Maye Gurbinsa a Ogun

  • Watanni hudu bayan rasuwar dan takarar gwamnan Ogun a inuwar PRP, jam'iyyar ta maye gurbinsa da wani
  • A watan Satumba, 2022 Allah ya yi wa tsohon dan takarar gwamnan PRP, David Bamgbose, rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Shugaban jam'iyar na jihar, Samsung Okusanya, ya bayyana Cyrus Johnson a matsayin sabon ɗan takarar gwamna a 2023

Ogun - Peoples Redemption Party (PRP) ta bayyana sunan Cyrus Johnson a matsayin dan takarar gwamna a jihar Ogun a zaben watan Maris mai zuwa 2023.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa PRP ta yi haka ne watanni hudu bayan tsohon dan takarar gwamnan da ta tsayar, David Bamgbose, ya riga mu gidan gaskiya.

Dan takarar PRP a Ogun.
2023: Watanni Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Mutu, PRP Ta Maye Gurbinsa a Ogun Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Mista Bamgbose ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya ta dan gajeren lokaci a watan Satumba na shekarar da ta gabata 2022.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

Shugaban jam'iyyar PRP reshen jihar Ogun, Samsung Okusanya, shi ya gabatar da Mista Johnson ga manema labarai a wurin wani takaitaccen taro da aka shirya a Abeokuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Okusanya ya bayyana cewa Johnson, wanda ya karanci ilimin Akawunta, ya zama dan takarar gwamna ne daga zaben fidda gwani wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta sa ido.

Mun shirya nasara a zabe mai zuwa - PRP

Ya kara da cewa jam'iyyar PRP ta shahara a lungu da sako kuma zata iya lashe zabe, "Saboda muna da wakilai a baki ɗaya gundumomi 236."

Da yake jawabi ga yan jarida, dan takarar gwamna a inuwar PRP yace idan aka zabe shi ya zama gwamna, gwamnatinsa zata fifita muradan talakawanta.

Daily Trust ta rahoto shi yana cewa:

"Muna fatan tafiyar gwamnatin da zata baiwa mutanenta fifiko saboda duk abinda zaka yi idan ba al'umma ne a sahun gaba ba to bai da amfani."

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Burtaniya ta gayyaci Atiku don wata ganawar sirri, an gano abin da suka zanta akai

"A Ogun abu na farko shi ne Noma, wanda zamu iya kira da samun yalwar abinci. Ya kamata a ce mun wuce matakin da sau ɗaya ake noma Masara. Ya kama kowa ya samu yalwar abinci."

EFCC ta bani hakuri - Okupe

A wani labarin kuma Tsohon Daraktan Kamfen Shugaban Kasa Ya Kubuta daga hannun EFCC Bayan DSS Ta Cafke Shi a Filin Jirgi

Tsohon DG na kamfen Peter Obi, Doyin Okupe, ya tabbatar da cewa ya bar Ofishin EFCC kuma manyan jami'ai sun ba shi hakuri.

A dazu ne dakarun DSS suka damke tsohon hadimin Jonathan a Filin jirgin MM dake Legas kuma suka mika shi hannun EFCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262