Mambobin PDP, APC da LP 2000 Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo

Mambobin PDP, APC da LP 2000 Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo

  • Mambobin APC, PDP, Labour Party sama da 2000 sun tattara sun koma jam'iyyar Accord a jihar Oyo
  • Rahoto ya nuna cewa jam'iyyun sun gamu da wannan koma baya ne yayin kamfen zagaye da yan takarar Accord suka shirya a Ibadan
  • Yan kasuwa da masu fatan Alheri ne suka cika tawagar zagayen, wasu da yawa sun tofa albarkacin bakinsu

Oyo - Akalla mambobi 2,000 na jam'iyyar APC, PDP da Labour Party ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar Accord Party a jihar Oyo.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an bayyana wannan ci gaban ne a wurin Ralin da gamayyar 'yan takarar Accord Party suka shirya a Ibadan, babban birnin jihar.

Zagayen neman kuri'a a Oyo.
Mambobin PDP, APC da LP 2000 Sun Sauya Sheka Zuwa Accord Party a Oyo Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Wadanda suka shirya Ralin sune, Injiniya Faozey Nurudeen, dan takarar Sanatan Oyo ta tsakiya, Akinjide Akinola, dan takarar majalisar wakilai a mazabar Egbeda/Ona-Ara da Olamide Ogundokun, dan takarar majalisar jiha a Egbeda.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a jihar APC yayin da dan majalisa ya sa sojoji suka farmaki 'yan PDP

'Yan takarar uku na Accord Party sun kara samun gagarumin goyon baya yayin Ralin zagaye Tituna domin tallata maɓufofinsu a birnin Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin zagayen kamfem, masu neman takarar sun ziyarci manyan wuraren kasuwanci a mazabar Egbeda/Ona-Ara inda suka fara daga yankin sawmill, Airport junction da sauransu suka roki alfarma.

Yadda yan takarar suka samu goyon baya daga mutane

Da suke zantawa da manema labarai yayin zagayen neman kuri'u, wasu daga cikin 'yan kasuwa sun yi bayanin dalilan da yasa suka mara wa 'yan takarar Accord Party baya.

Daya daga cikin 'yan kasuwan yankin yace:

"Muna bukatar matasa masu hazaka kamar wadan nan biyun su karbi shugabanci a jihar Oyo. Amma ba wanda ya yi watsi da su ba tun da aka zabe shi a 2019."

Wata yar kasuwan daban ta yi bayanin cewa:

Kara karanta wannan

Ribas: ‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da Yayi wa Mata 10 Ciki

"Eh ina kaunar Faozey, matashi ne mai jini a jika, shin kun san Akinjide Kazeem Akinola na da Ofishin kamfe kusa da shagona kuma ya na samu alfahari a yankin ba ya takura wa kasuwancin mu kamar wasu."
"Da wannan kadai ya gamsar, muna goyon bayansa kuma muna kokarin jawo hankalin mutanen mu su jefa wa Accord kuri'unsu idan zabe ya zo."

A kwanakin baya, Jaridar Daily Post ta rahoto Shugaban Accord Party na kasa na ikirarin cewa jam'uyyarsa zata ba da mamaki a babban zabe mai zuwa.

Na kusa da gwamnan Enugu ya koma bayan Obi

A wani labarin kuma Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

Hadimin gwamnan Enugu, Emmanuel Jonathan, ya yi fatali da Atiku, ya fito fili ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi na Labour Party.

Mai taimaka wa gwamnan kan midiya, Mista Jonathan yace yana nan daram a PDP amma yana tare da Obi. Gwamna na cikin yan G5.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262