Hadimin Gwamna Ugwuanyi Ya Raba Gari da Atiki, Ya Koma Bayan Obi a 2023
- Mai taimakawa gwamnan jihar Enugu kan harkokin midiya ya fito ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi
- Emmanuel Jonathan yace ba zai zauna shiru ba dole ya kara muryar a bayan mai neman zama shugaban kasa na LP
- Gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, na daya daga cikin tawagar G5 dake takun saka da Atiku Abubakar
Enugu - Hadimin Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Emmanuel Jonathan, ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar Labour Party (LP), Peter Obi, gabanin babban zaben 2023.
Mista Jonathan, babban mai taimakawa gwamna kan harkokin midiya ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Gwamna Ugwuanyi na daya daga cikin gwamnoni 5 da suka fusata suka ware kansu a jam'iyyar PDP ana kiransu da tawagar gaskiya ko G-5 karƙashin Nyesom Wike na Ribas.
Meyasa ya bar Atiku ya koma wurin Peter Obi?
Jonathan ya kara da bayanin cewa ba zai ci gaba da gimtse bakinsa yana kallo ana lalata shugabanci, ya jaddada cewa ya zabi ɗaga muryarsa don goyon bayan burin Peter Obi/Datti Yusuf Baba-Ahmed.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Najeriya na fama da gurbataccen shugabanci wanda ya jefa da yawan mutanen da ba su ji ba basu gani ba cikin kakaniyakayi duk da suna a raye."
"Hanya daya da za'a magance wannan yanayi ita ce dole a duba wadan nan kalmomin, gaskiya, gogewa, adalci da daidaito yayin zaben wadanda zasu ja ragamar harkokin Najeriya a shekaru hudu masu zuwa."
Ya kuma bayyana cewa yana nan daram a matsayin mamban jam'iyyar PDP duk da ya ayyana cikakken goyon bayansa ga dan takarar LP ya aje Atiku Abubakar.
PDP da APC duk sun saɓa wa adalci - Jonathan
Hadimin gwamnan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda PDP ta karya tsarin mulkin karba-karba wanda ya kunshi kudu maso gabashin Najeriya ya samar da shugaban kasa a 2023.
Ya ce abun ba dadi yadda PDP ta shiga gaba a cikin manyan jam'iyun da suka yi fatali a tsarin karba-karba.
Bugu da kari Mista Jonathan ya caccakin APC bisa gaza zakulo ɗan takarata daga kudu maso gabas da kuma tsaida takara Musulmi da Musulmi.
A wani labarin kuma Ta Karewa Tinubu a Arewa, Jiga-jigai da Mambobi 30,847 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
Jiga-jigai da 'yan siyasa sama da 30,000 daga APC da wasu jam'iyyu sun sauya sheka zuwa PDP a Sandamu da Mai'adua, jihar Katsina.
Tsohon sakataren gwamnati, Mustapha Inuwa, ya roki dandazon magoya baya da su kawar da APC domin ita ta kawo musu wahalar rayuwa.
Asali: Legit.ng