Kotun Koli Zata Raba Gardama Kan Halastaccen Dan Takarar APC a Jigawa
- Daga karshe dai Kotun daukaka kara ta shirya tsaf don kawo karshen rikicin tikitin gwamnan Jigawa na APC
- Kwamitin Alkalai 5 a zaman ranar Laraba sun zabi ranar 13 ga watan Janairu domin kawo karshen shari'ar
- Adamu Aliyu ne ya daukaka kara har zuwa Kotun koli yana kalubalantar sahihancin zaben Umar Namadi
Abuja - A yau Laraba, Kotun Koli ta dage zama zuwa ranar Jumu'a 13 ga watan Janairu domin yanke hukuncin karshe kan rigingimun tikitin takarar gwamnan jihar Jigawa a inuwar APC.
Kwamitin Alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Okun ne ya zabi ranar yanke hukuncin bayan sauraron kowane bangare, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Farouk Adamu Aliyu, shi ne ya daukaka karar zuwa Kotun Koli inda ya kalubalanci nasarar Umar Namadi, mataimakin gwamna.
Umar Namadi ta hannun lauyansa, Prince Lateef Fagbemi, ya samu nasara kan shari'ar a babbar Kotun tarayya dake zama a Dutse da kuma Kotun daukaka kara mai zama a Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma a karar da ya shigar gaban Kotun Allah ya isa mai lamba SC/1453/2022, Adamu Aliyu ya kalubalanci hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba.
Yadda Kotunan baya suka yanke hukunci
Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Ita Mbaba na Kotun daukaka kara a Kano ya yi fatali da karar Adamu Aliyu kana ya tabbatar da nasarar Umar Namadi a matsayin dan takarar APC.
Kwamitin ya yi watsi da karar wacce Aliyu ya shigar yana mai kalubalantar hukuncin Babbar Kotun tarayya mai zama a Dutse karkashin mai shari'a Hassan Dikko.
Tun farko mai shari'a Dikko ya yanke cewa Aliyu ba shi da hurumin shigar da kara kan batun kuma ya gaza gamsar da Kotu da sahihan shaidu.
Yadda zaman yau a Kotun Koli ya gudana
A zaman yau Laraba, Lauyan mataimakin gwamnan Jigawa ya roki Kotu ta yi fatali da karar Adamu Aliyu kana ta tabbatar masa da hakkinsa na zama dan takarar APC.
A na shi bangaren Lauyan Adamu Aliyu ya musanta zancen kana ya roki Kotun ta amince da rokon wanda yake kare wa, kamar yadda PM News ta ruwaito.
A wani labarin kuma Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar da NNPP ta Shigar da Uba Sani da yan takarar majalisar jiha 34
Kotun daukaka kara mai zama a Kaduna ta yi fatali da karar da jam'iyyar NNPP mai kayan dadi ta shigar da APC da INEC.
NNPP da dan takararta sun nemi Kotun ta soke tikitin takarar Uba Sani da sauran yan takarar majalisar jiha 34 na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng