APC da Wasu Jam'iyyu Sun Rasa Mambobi Sama da 30,000 a Jihar Buhari
- Jam'iyyar APC a Katsina da wasu jam'iyyu sun yi gagarumin rashi na dubbannin mambobinsu a kananan hukumomi 2
- Jiga-jigai da mambobi sama da 30,000 na jam'iyyu daban-daban ne suka sauya sheka zuwa PDP a shiyyar Buhari
- Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, yace lokaci ya yi da Katsinawa zasu kawar da mulkin APC
Katsina - Mambobi 30,847 na jam'iyar APC mai mulki da wasu jam'iyyu sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar Adawa watau PDP a jihar Katsina.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan siyasan da suka sauya shekan sun fito ne daga kananan hukumomin Sandamu da Mai'Adua bisa jagorancin Danjuma Shu'aibu.
Tsohon sakataren gwamnatin Katsina kuma Darakta Janar na Kamfen Atiku/Lado, Mustapha Inuwa, ne ya tarbi mutanen yayin da jirgin yakin neman zaben PDP ya dira Mai'Adua da Sandamu ranar Laraba.
Da yake jawabi ga dumbin magoya bayan da suka halarci Ralin, Inuwa ya ce daga cikin masu sauya shekar harda fitattu kuma jiga-jigai a Sandamu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ambaci sunayensu da, Alhaji Sha'aibu Danjuma, Maamuda Ado, Sabiu Uli da kuma Maria Lawal, shugabar matan yankin da dai sauran su.
Tsohon Sakataren ya yaba wa dubbannin masu sauya shekar bisa watsi da APC imda ya kira matakin da suka dauka da wayewa.
Bugu da kari, Inuwa ya yaba da yadda jama'a suka fito kwansu da kwarkwata domin tarban dan takarar gwamna na PDP, Yakubu Lado, dan takarar Sanatan Shiyyar Daura, Babba Kaita, da sauran yan takarar PDP.
Inuwa ya ce:
"Kun zo nan ne bisa ra'ayin kanku, bamu tilasta ko dauko hayar kowa ba kamar yadda APC take yi amma kun zo ne saboda kauna da yardarku ga PDP."
"Muna rokon karku gajiya wurin fatattakar gwamnatin APC da ta kawo mana wahalar rayuwa tsawon shekaru Bakwai da suka gabata, idan zabe ya zo ku kore su."
"Muna tabbatar muku cewa duk wannan wahalar da tsadar rayuwa da mukae fama da ita zata wanye nan da kwanaki 44 masu zuwa."
Mamban PDP a Katsina, Ƙabir Abdullahi, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa wannan ba karamin goyon baya bane da PDP ta samu.
Matashin dan siyasan ya ce duk da bai je wurin ba ya san taro ya yi kyau. Da aka tambaye shi ko ya zasu ji da rigingimun cikin gida, Abdullahi ya ce:
"Ba'a cin nasara sai da kalubale, duk wannan rigimar ta manyan mu a Katsina alama ce ta nasara kuma zasu zo su hada kai zaka ce ni na fada maka haka, zaben saura kwana nawa ne?"
Amma wani jigo mai rike da mukami a PDP ta karamar hukumar Danja, ya ce zai wahala jam'iyyar adawa ta iya kai bantanta a zabe mai zuwa.
Dan siyasan, wanda ya nemi a sakaya bayanasa, yace rikicin da ke faruwa tun daga uwar jam'iyya zuwa nan matakain jiha, shi ne ya faru a 2014.
Kotun Allah Ya Isa Zata Yanke Hukuncin Karshe Kan Halastaccen Dan Takarar APC a 2023
A wani labarin kuma Kotun Koli ta zabi ranar 13 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan rigimar tikitin takarar gwamnan jigawa a APC
Kotun Koli a Najeriya ta zabi ranar Jumu'a mai zuwa domin raba gardama kan dambarwar tikitin takarar gwamnan Jigawa na APC. Farouk Adamu Aliyu ya ki yarda da hukuncin Kotun tarayya da kotun daukaka kara, ya zarce Kotun da ake wa lakabi da daga ke sai Allah ya isa.
Asali: Legit.ng