Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba
- Bola Ahmed Tinubu yana ganin har zuwa yanzu, ba za a ce an gama magance matsalolin tsaro ba
- Harin da aka kai a filin jirgin kasa a jihar Edo ya jawo Tinubu ya sha bam-bam da shugaban Najeriya
- Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo zaman lafiya, kuma ya ce ya cika alkawarin da ya dauka
Abuja - A wurin Bola Ahmed Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, har yau ana fama da matsalar rashin tsaro.
Premium Times ta rahoto Bola Ahmed Tinubu yana kokawa da harin da aka kai a tashar jirgin kasa na iguben, inda aka yi gaba da fiye da mutane 30.
A wani jawabi da ya fitar ta bakin Hadiminsa, Tunde Rahman, ‘dan takaran shugaban kasar ya yi Allah-wadai da wannan harin da ‘yan ta’adda suka kai.
Bola Tinubu ya yi amfani da damar wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da na jihar Edo su hada-kai wajen ceto duk mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rahoton ya ce tsohon gwamnan na jihar Legas wanda ya saba bada kariya ga gwamnatin APC ya fito yana cewa harin ya nuna akwai sauran aiki.
‘Dan takaran kujerar shugabancin kasar ya ce garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suka yi, ya tabbatar da ba a gama samun nasara kan ta’addaci ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma ‘dan siyasar ya ba mutane kwarin gwiwar cewa za a kawo karshen aika-aikar nan, ya kuma nemi gwamnati mai-ci ta saci amsa daga manufofinsa.
Amma za mu ci nasara - Tinubu
"Wannan tunatarwa ce cewa ba mu kammala yin nasara a wajen yaki da rashin tsaro ba, kuma har yanzu akwai ‘yan tada zaune tsaye da ke barna.
Amma ina so in tabbatarwa mutanen Najeriya za muyi nasara a wannan yakin."
- Bola Tinubu
Na cika alkawura na - Buhari
Hakan yana zuwa ne a lokacin da Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari yake cewa ya cika duka alkawuran da ya dauka a lokacin da yakin zabe.
Muhimman alkawun da Buhari ya yi sun shafi inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki da yaki da rashin gaskiya, da yake jawabi a Yobe, ya ce ya ci nasara.
Alkawarin Tinubu a gaban Buhari
Da aka je wajen yakin neman zabe a Damaturun jihar Yobe, an ji labari Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen yajin aikin da ‘Yan ASUU suke yi.
Idan ya zama magajin Buhari a Mayun 2023, ‘dan takaran ya yi alkawarin zai rika ba daliban jami'o'in Najeriya rancen kuɗi domin suyi karatu da sauki.
Asali: Legit.ng