Rikicin PDP: Gwamnonin G5 Sun Goyi Bayan Atiku A Sirrance? Sabbin Bayanai Sun Bayyana
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi watsi da rahoton cewa shi da sauran gwamnonin G-5 sun goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar
- Terver Akase, mai magana da yawun Gwamna Ortom cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya ce masu yada wannan labarin suna yi ne don dalili na siyasa
- Ortom ya bayyana wannan rahoton a matsayin labarin kanzon kurege, da aka kirkira don kunyata gwamnonin bisa gwagwarmayar da suke yi
Makurdi, Benue - An yi watsi da ikirarin cewa gwamnonin da ke fushi da jam'iyyar Peoples Democratic Government, PDP, sun yarda kuma sun amince su goyi bayan takarar dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar.
Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai, Terver Akase, ya yi watsi da ikirarin a ranar Talata, 10 ga watan Janairu, The Punch ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnonin na G-5 sun yi magana kan goyon bayan Atiku Abubakar a sirrance
Gwamnonin da ke fushi da jam'iyyar PDP wadanda aka fi sani G-5 da suka hada da Ortom, Seyi Makinde (Oyo), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Nyesom Wike (Rivers) da Okezie Ikpeazu (Abia).
Sun nisanta kansu daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku har sai an cika musu ka'idarsu na tsige Iyorchia Ayu, wanda shine shugaban jam'iyyar na kasa.
Sai dai wata rahoto na shafin intanet ta yi ikirarin cewa kungiyar na G-5 sun yarda za su goyi bayan dan takarar shugaban kasar na PDP.
Bayani na baya-baya game da PDP, gwamnonin G5, Nyesom Wike, Atiku Abubakar, Samuel Ortom, Zaben 2023
Akase ya bayyana rahoton a matsayin tatsuniya da aka kirkira da nufin kunyata gwamnonin na G5 da suka zabi neman ganin an musu adalci, gaskiya da daidaito.
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa masu yada labarin kawai suna neman cimma wata manufa ce tasu ta siyasa, shi yasa suka gaza fadin inda gwamnonin suka hadu kuma suka cimma wannan shawarar.
Wani sashi na sanarwar ya ce:
"Marubutan suna son amfani da damar rikicin da ke faruwa a PDP din ne don cimma manufansu. Gwamna Ortom da wasu mambobin G5 ba su goyi bayan dan takarar shugaban kasar ba."
Gwamna Mohammed Ya Bayyana Abin Da Ya Hada Shi Da Gwamonin G5
A wani rahoton, Gwamna Bala Muhammad, ya ce abu daya kacal ya hada shi da gwamnonin tawagar G5 da ke fushi da shugabancin jam'iyyar PDP karkashin Gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
G5 din ta kunshi Wike, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, Ugwuanyi na Enugu, Seyi Makinde na Oyo.
Asali: Legit.ng