Jam'iyar APC Ta Rasa Kaso 70 Na Magoya Bayanta a Arewa, Jibrin
- Kakakin kamfen jam'iyyar NNPP mai kayan marmari yace APC ta rasa sama da kaso 70 na masu kaunarta a arewacin Najeriya
- Abdulmumin Jibrin yace tuni Kwankwaso ya kwace dukkanin wannan goyon baya kuma zai ci zabe ya zama shugaban kasa
- Tsohon dan majalisar wakilan tarayyan ya bar APC ne bayan samun sabani da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
Abuja - Abdulmumin Jibrin, mai magana da yawun kwamitin kamfen New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ce APC zata sha wahala a babban zaben watan Fabrairu mai zuwa.
Jibrin ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da kafar Talabijin ta Channels tv ranar Litinin 9 ga watan Janairu, 2023.
Yace a yanzun duk kaunar da ake wa jam'iyya mai mulki a baya a arewacin Najeriya ya koma wurin Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP.
Tsohon dan majalisar tarayya daga Kano ya kara da cewa PDP da APC na tsaka mai wuya a kan siradin rushewa, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kakakin NNPP ya ce Kwankwaso zai lashe dukkan kuri'un Kanawa kuma ya ci zabe da nasarar raba ni da yaro, a cewarsa babu wani dan takarar shugaban kasa da zai samu kaso 25% a Kano.
Jibrin ya ce:
"Duk lokacin da APC zasu yi hasashe kan PDP suna cewa ta rasa Kwankwaso, ta rasa Peter Obi, ta rasa gwamnoni 5. Tabbas PDP na cikin rigingimu amma ba ita kadai ba APC kanta tana cikin yanayi mai kalubale da wahala."
"Kuri'u miliyan 12m da suke taƙama da su yanzu ta fece, a halin da ake ciki yanzu, jam'iyyar APC ta rasa kaso 70 zuwa 80 cikin 100 na magoya bayanta a arewacin Najeriya."
"Idan Kwankwaso ya lakume kuri'un arewa musamman arewa maso yamma da karin wadanda zai tsakuro a kudu inda yake kara karbuwa, NNPP zata samu nasara a zabe mai zuwa."
Har watan Mayu, 2022 tsohon dan majalisar tarayyan ya kasance mamba a APC kuma darakta janar da kungiyar masoyan Bola Ahmed Tinubu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Jibrin ya yanke barin APC ne bayan sabani ya shiga tsakaninsu da Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano.
NNPP zata fara kamfen Kwankwaso
A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Kano ya kaddamar da tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP
Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iya mai kayan daɗi, Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai fara kamfe a jihar Bauchi ranar 12 ga watan Janairu.
Da yake kaddamar da PCC-NNPP, Kwankwaso ya roki yan Najeriya masu fatan alheri su hada hannu da shi don ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng