Tsohon Gwamnan Adamawa Bindow, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Tsohon Gwamnan Adamawa Bindow, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

  • Tsohon gwamna da ya sauka na jihar Adamawa, Sanata Jibrilla Bindow ya canza sheka daga APC zuwa PDP gami da marawa gwamna Umaru Fintiri baya don ya zarce
  • Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne ta wakilai 250 na shugabannin kungiyoyin dake mara masa baya a ranar Litinin
  • Sun bayyana yadda uban gidansu ya aukesu su isar da sakon godiyarsa ga Fintiri bisa kammala kwangilolin da ya gada, tare da goya masa da Atiku baya a tafiyarsu

Adamawa - Tsohon gwamnan jihar Adamawa wanda bai jima da sauka ba, Sanata Jibrilla Bindow ya canza shekarsa zuwa jam'iyyar PDP, kuma yanzu yana marawa gwamna Umaru Fintiri bayan don ya zarce, Channels TV ta rahoto.

Jibrilla Bindow
Tsohon Gwamnan Adamawa Bindow, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan, wanda a baya 'dan jam'iyyar APC ne, ya sanar da hakan ne ga gwamna Fintiri ta wakilcin shugabanni 250 na kungiyoyin dake goya masa baya.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilin Da Ya Sa Muka Tsayar da Mataimakina Takara a APC, Ganduje

Yayin jawabi a dakin taron Banquet na gidan gwamnatin Yola a ranar Litinin, shugaban wakilan, Abdullahi Bakari ya ce ziyarar bisa umarnin uban gidansa ne.

A cewar shugaban, tsohon gwamnan ya umarcesu da su isar da sakon jinjina ga gwamna Fintiri bisa tabbatar da karasa kwangilolin da ya gada a fadin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika, suna goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda a cewarsu, shugaba ne garesu tsawon shekaru, don haka yana bukatar su goya masa baya a tafiyarsa ta neman shugabancin kasa.

Buhari ya kaddamar da kamfen din Binani da Tinubu a Adamawa

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wanki kafa inda ya dira har jihar Adamawa a ranar Litinin da ta gabata inda ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben Aisha Binani da Bola Ahmed Tinubu a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran Jin Wanda G5 Zasu Goyi Baya, Sabuwar Rigima Ta Bullo PDP a Arewacin Najeriya Kan Atiku

Ya daga hannun Aisha Binani inda ya bukaci jama'ar jihar Adamawa da su zabe ta tare da kafa tarihi don ta zama mace ta farko da aka zaba matsayin gwamna a Najeriya.

A bangarenta, Sanata Aisha Binani ta sha alwashin biyan albashi da fansho matukar ta dare wannan kujerar mafi daraja ta jihar Adamawa a matsayin gwamnan jihar.

Gogaggiyar 'yar siyasar dai ta lallasa Malam Nuhu Ribadu tare da Sanata Jibrilla Bindow inda tayi caraf da tikitin takarar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel