Kano: Ganduje Ya Bayyana Biyayya Da Wasu Dalilai 3 Da Suka Sa Gawuna Ya Zama Dan Takarar APC
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya magantu a kan dalilin da yasa suka tsayar da Nasir Gawuna a matsayin wanda suke so ya gaje shi a 2023
- Ganduje ya ce suna son mutumin da ya san manufofinsu ta yadda zai daura daga inda suka tsaya
- Ya ce sun zabi Gawuna ne saboda kwarewarsa, biyayya, sanin kan aiki da kyakkyawar mu'amalarsa da mutane da dama
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin da yasa Nasir Gawuna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.
Jahar Kano na daya daga cikin jihohi masu zafi idan aka zo maganar zabe don kowace jam’iyya na mayar da hankali kan jihar ne saboda karfinta a zabe.
Gawuna shine mataimakin gwamnan jihar Kano mai ci kuma shine zai daga tutar jam’iyyar APC a zaben gwamna na watan Maris a jihar.
Yayin da yake jawabi a wani taron hada kudi da abokan Gawuna suka shirya a Abuja a ranar Litinin, Ganduje ya bukaci mutane da su zabi dan takarar don tabbatar da ci gaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ganduje ya bayyana cewa Gawuna ya zama dan takarar gwamnan APC ne saboda karbuwarsa, biyayya, ilimi, gogewa da kuma alakarsa da mutane, Daily trust ta rahoto.
Babu mai iya kayar da Gawuna a zaben gwamnan Kano, Ganduje
Gwamnan ya ce babu wata jam’iyyar siyasa a Kano da za ta iya kayar da Gawuna.
Wani bangare na jawabin na cewa:
“Wani abu guda da muka yi la'akari da shi shine ci gaban ayyuka saboda yana da matukar muhimmanci a harkokin shugabanci; ci gaba a shirye-shirye, da gine-gine saboda bayan gina tubali mai karfi ana bukatar wanda zai ci gaba daga inda aka tsaya.
“Dr Gawuna na sane da tsare-tsare da ayyukanmu kuma mun yarda cewa ci gaba da aiki. Kuma wannan irin rainon da muke yi. Wadanda za su ci gaba da aikin raya al'umman da aka kafa. Muna mutunta haka kuma Insha Allah, Za mu ci gaba da dorawa a kan haka.”
Zan yi amfani da kwarewata wajen yiwa Kanawa hidima, Gawuna
Da yake jawabi a nasa bangare, Gawuna ya ce ci gaba daga inda gwamnatin baya ta tsaya shine sirrin samun kyakkyawan sakamako, rahoton Aminiya.
Gawuna ya ce:
"Sanin kan aikina na da muhimmanci sosai, kuma a shirye nake na yi amfani da ilimina na tsawon shekaru wajen hidimtawa jiharmu."
Asali: Legit.ng