Dole Shugaban Kasar Nigeria Ya Fito Daga Kudancin Kasar Nan Inji Akeredolu

Dole Shugaban Kasar Nigeria Ya Fito Daga Kudancin Kasar Nan Inji Akeredolu

  • Kwanaki 46 ya rage a jefa kuri'a a akwatunnan zabe a Nigeria dan fitar da shugaban kasar da zai shugabanci Nigeria tsawon shekara 4
  • Gwamnan jihar Ondo yace dole ne fa ba lallashi shugaban kasar Nigeria sai ya fito daga yankin kudancin Nigeria
  • Ba batun ace wai shugabncin kasar nan yanki daya ne zai ringa yi, dole a samu sauyi ko kuma canji in ana son zaman lafiya

Ondo - Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce indai ana san adalci da tsari na gaskiya dole shugaban kasar Nigeria na gaba ya kasance daga yankin kudancin kasar nan.

Gwamnan yana fadar wannan maganar a lokacin da yake gabatar da ibada a majami'ar RCCG 22 dake Akere dan tuna ranar sojoji ta Nigeria, Rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

Akeredolu
Dole Shugaban Kasar Nigeria Ya Fito Daga Kudancin Kasar Nan Inji Akeredolu Hoto: Premiun Times
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan yace mun gabatar da wannan bikin ne dan jajantawa da kuma taya iyalai da yan Nigeria da suka rasa 'yan uwa da suke aikin soja dan kare kasar mu.

Gwamnan yace:

"ina sane da yadda matsal-tsalun tsaro suka dabaibaye kasar nan da kuma yadda ake rasa rayuka a kullum."

Ba gudu ba ja da baya game da batun shugaban kasa ya fito daga yankin kudancin kasar nan

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Gwamnann Ondo yayi makamancin wannan fruruncin a ranar Alhamis din nan yana mai cewa ba gudu ba ja da baya kan batun samar da shugaban kasa da kudancin kasar nan.

Akeredolu ya roki yan Nigeria da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Nigeria.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

Gwamnann yace bayan shugaba Muhammadu Buhari ya gama shekaru takwas ba wanda ya kamata ace an zaba sai dan kudan cin kasar nan.

Batun karba-karba a tsakanin jam'iyyu

Batun karba-karba dai a tsakanin jam'iyyu na samun cikas, musamman ma ga wanda yake kan kujerar da ake batun karba-karba din.

Misali a shekarar 2015 jam'iyyar PDP ta dage sai mulki ya dawo Arewa, inda kuma shugaban kasar lokacin Goodluck Jonathan ya dage kan sai ya koma, wannan ya janyo tsagewar wasu gwamnoni da suka sawa kansu sunann G7

ko a yanzu ma jam'iyyar APC ta so gabatar da wannan tsarin sai dai ba'a je ko ina ba batun ya turnuke jam'iyyar da sai da yasa aka bar kowa ya fito takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel