Fasto Ya Rabu da Harkar Addini, Ya Fito Neman Gwamna Gadan-Gadan a Jam’iyyar APC
- Rabaren Hyacinth Alia ya bayyana dalilin shi na rungumar siyasa domin ya zama Gwamnan Benuwai
- Malamin addinin shi ne ‘Dan takarar kujerar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa
- Alia ya kaddamar da manufofinsa a Makurdi, yake cewa yana takara ne domin ya ceci mutanensa
Benue - Rabaren Hyacinth Alia ya yi karin-haske a kan abin da ya kai shi ga tsayawa neman takarar kujerar Gwamnan jihar Benuwai a zaben shekarar nan.
Punch ta ce Hyacinth Alia ya bayyana wannen a lokacin da ya gabatar da manufofinsa gaban manema labarai a birnin Makurdi da ke jihar Benuwai.
Hyacinth Alia ya jaddada cewa akwai bukatar a canza halin talaucin da al’ummar Benuwai suke ciki, a dalilin wannan ne ya fito neman Gwamnan jihar.
A jawabin da ya yi a ranar Lahadi, 8 ga watan Junairun 2022, an ji Faston yana cewa bai kamata Benuwai ta zauna a cikin takauci ba domin tana da arziki.
Benuwai tana da baiwar arziki
"Benuwai ta na da arzikin da bai kamata tayi talauci ba, wannan kin godewa ni’imar da Ubangiji ya yi mana ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatina za ta zauna ne a kan turaku bakwai – muhimman cikinsu su ne tsare rayuka da dukiyar al’umma.
- Hyacinth Alia
Alia zai bunkasa noma da kiwon lafiya
The Cable ta rahoto Alia yana cewa ya zo da dabarun da zai magance matsalar tsaro ta hanyar hana kiwo a foli, sannan ya yi amfani da fasahar zamani.
Limamin katolikan da ya koma ‘dan siyasa ya ce zai inganta duk wani dakin shan magani da asibitocin gwamnati ta yadda mata za su haihu a kyauta.
Idan ya zama Gwamna Rabaren din ya ce zai maida hankali a kan harkar noma, raya karkara, kasuwanci, kimiyya da fasaha da kuma cigaban al’umma.
‘Dan takaran na jam’iyyar APC ya kuma yi alkawarin gwamnatinsa za ta rika tafiya da kowa, an rahoto shi yana cewa wadanda su ke mulki ba su dace ba.
Idan aka zabe shi a Fubrairun nan, Alia ya yi alwashin za a dage wajen noma kamar yadda aka san jihar a 1983, har aka yi mata lakabi da kwandon Najeriya.
Kuri'un APC a jihar Yobe
Ku na da labari cewa tsohon gwamna Ibrahim Gaidam da Sanata Ahmad Lawan su ne shugabannin kwamitin neman zaben Jam’iyyar APC a 2023 jihar Yobe.
Da ake rantsar da kwamitin takarar, Ahmad Lawan ya nuna tun da Kashim Shettima yana takara, ya kamata mutanen Yobe su ba APC akalla 98% na kuri’unsu.
Asali: Legit.ng