Ba Zamu Kwancewa Juna Zani a Kasuwa da Shettima Ba Kamar Yadda Obasanjo Suka Yi da Atiku, Tinubu

Ba Zamu Kwancewa Juna Zani a Kasuwa da Shettima Ba Kamar Yadda Obasanjo Suka Yi da Atiku, Tinubu

  • Gabannin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya shirya wani taron matasa a Abuja
  • Da yake jawabi a wani taro, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya caccaki tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Atiku ABubakar
  • Tinubu ya ce shi da abokin takararsa, Kashim Shettima, ba za su kwancewa juna zani a kasuwa kamar yadda Obasanjo da mataimakinsa suka yiwa juna a kasuwar Wuse ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin cewa shi da abokin takararsa, Kashim Shettima, za su ci gaba da hulda mai kyau idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya fada ma yan Najeriya cewa ba zai yi shugabanci mai cike da rigingimu irin wanda aka yi tsakanin shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abubakar tsakanin 1999 da 2007 ba, inda suka kwancewa juna zani a kasuwa.

Kara karanta wannan

Mubaya’ar da Obasanjo Ya yi wa Peter Obi Ta Jawo Bola Tinubu ya Tona Masa Asiri

Bola Tinubu
Ba Zan Yaki Shettima Kamar Yadda Obasanjo Ya Yaki Atiku Ba – Tinubu Ya Dauki Alkawari Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 6 ga watan Janairu, yayin wani taron matasa da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya shirya a Abuja, jaridar This Day ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ni da Shettima ba za mu kwancewa juna zani a kasuware Wuse kamar yadda Obasanjo da Atiku suka yi ba. Ba na son fadin wannan amma babu yadda na iya."

Taron ya samu halartan manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki da suka hada da Gwamna Simon Lalong (Filato), Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano) da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Tinubu ya yiwa matasa alkawarin samun bashi, babu yajin aikin ASUU

Tinubu ya kuma yiwa matasa alkawarin, cewa za su taka muhimmiyar rawar gani a gwamnatinsa.

Ya basu tabbacin cewa yajin aiki da kungiyar malaman jami'o'i ke yawan tafiya zai zama tarihi. A cewarsa, "shekaru hudu zai zama shekaru hudu."

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce Ba Za a Gani a Kasa Ba, Tinubu Kan Alkawaran Zaben da Atiku da PDP Suka Daukarwa Yan Najeriya

Dan takarar na APC ya kuma yi alkawarin cewa akwai bashin da za a baiwa dalibai da ke bukata sannan su biya idan suka fara aiki da samun karfin iya biya.

Tinubu ya roki matasa a kan su zabe shi, yana mai cewa ba za su yi danasanin haka ba.

A wani labarin kuma, Bola Tinubu, ya radawa abokin hamayyarsa na Labour Party. Peter Obi suna 'Mr Stingy' wato mai mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng