2023: Zan Lallasa Tinubu, Atiku, Obi Da Sauran A Babban Zabe, In Ji Ƴar Takarar Shugaban Ƙasa Mace

2023: Zan Lallasa Tinubu, Atiku, Obi Da Sauran A Babban Zabe, In Ji Ƴar Takarar Shugaban Ƙasa Mace

  • Yar takarar shugaban kasa tilo a babban zaben shekarar 2023, Chichi Ojei, ta jam'iyyar APM ta ce za ta lallasa, Atiku, Tinubu, Obi da sauransu
  • Ms Ojei ta sanar da hakan ne cikin sakonta na sabon shekara ga yan Najeriya tana mai cewa karuwar mata da matasa a harkar siyasa yasa ta samu kwarin gwiwa cewa za ta yi nasara
  • Yar takarar shugaban kasar na APM ta ce yan Najeriya na da daman yantar da kansu na gaskiya ta hanyar zaben yan takarar da suka dace a 2023

FCT, Abuja - Chichi Ojei, yar takarar shugaban kasa na jam'iyyar Allied People’s Movement (APM) ta ce tana da kwarin gwiwa cewa za ta lashe zaben shugaban kasa na watan Fabrairu.

Ms Ojei ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a wani sakon sabon shekara ga yan Najeriya, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ana Zaman Jiran Zabin G5, Atiku da PDP Sun Yi Babban Kamu a Jihar da APC Ke Mulki

Ms Ochei
Zaben 2023: Zan Kada Tinubu, Atiku, Obi Da Sauran, In Ji Ƴar Takarar Shugaban Ƙasa Mace. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akwai yan takarar shugaban kasa 18 da za su fafata a babban zaben na 2023.

Ms Ojei ce mace tilo cikin yan takarar shugaban kasar na 2023, kuma tana ganin za ta iya cin zaben.

Ina kira ga mata da matasa su zabi jam'iyyar APM a zaben 2023 - Ochei

Ta ce:

"Duba da karuwar matan Najeriya da matasa, ni ne na fi daman yin nasara a babban zabe fiye da sauran yan takarar.
"A yayin da muke tunkarar zabe mafi tarihi a siyasar Najeriya, ba sirri bane cewa yawan mata da matasa ya karu sosai.
"Ina kira ga yan Najeriya wadanda suka isa yin zabe, su karbi katinsu na PVC, musamman mata da matasa, su zabi jam'iyyar Allied Peoples Movement.
"Ni ce kadai yar takara mace kuma daya cikin mafi kananan shekaru da ke takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 na Najeriya kuma duk kuri'an da aka jefa min, kuri'a ce ga makomar Najeriya."

Kara karanta wannan

Ko Tinubu Yana Taba Kirifto Ne: Yasha Alwashin Taimakon Yan Kirifto In Ya Kai Ga Gaci

A cewar Ms Ojei, zaben da ke tafe wani dama ne ga yan Najeriya su yi yaki don samun yancin kasar na gaskiya.

Ta ce idan yan Najeriya sun zabi wadanda suka dace, za su samu ikonsu na fadin albarkacin baki, taro, walwala, daidaito da adalci kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164