Hotuna: Buhari ya Gana da 'Yar Takarar Gwamnan Adamawa ta APC a Fadar Aso Villa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da 'yar takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC
- Aishatu Binani ta ziyarci shugaban kasan a fadarsa da ke Abuja a ranar Juma'a inda ta samu rakiyar wasu jiga-jigan jam'iyyar na kasa
- A watan Nuwamba ne dai kotun daukaka karar ta dawo da Aisha Binani a matsayin sahihiyar 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar APC
Aso Villa, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya karba bakuncin Aishatu Binani, 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC, a fadarsa da ke Aso Rock a Abuja ranar Juma'a.
Abdullahi Adamu, shugaban jami'iyyar APC mai mulki na kasa da Pauline Tallen, ministan harkokin mata, duk sun hallara yayin taron.
A watan Nuwamba, kotu daukaka kara da ke zamaa jihar Adamawa ta dawo da Binani matsayin 'yar takarar kujerar gwamnan APC a jihar, bayan wata kotun tarayya ta fattatake ta a watan Oktoba.
Ga wasu daga cikin hotunan:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda shafin @OfficialAPCNg ya wallafa a Twitter, Binani ta gana da Buhari tare da jiga-jigan jam'iyyar APC na kasa.
Binani ta ga samu, ta ga rashi
Aisha Binani ita ce ta kasance gwarzuwar macen da ta lashe zaben fitar da gwanin 'dan takara na jam'iyyar APC a jihar Adamawa inda ta lallasa Malam Ribadu, wanda ya taba shugabantar EFCC da tsohon gwamnan da ya gabata na jihar Adamawa, Bindow.
Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, Malam Nuhu Ribadu ya maka ta a gaban kotu inda wata babbar kotun tarayya ta kwace takarar ta tare da bayyana cewa APC ba ta da 'dan takarar gwamna a jihar Adamawa.
Kotun daukaka kara ta dawowa da Binani takarar ta
Sai dai a hukuncin kotun daukaka kara da ta yanke kan zaben fitar da gwanin, ta ayyana Binani matsayin halastacciyar 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2023.
Ribadu ya hakura, yace ba zai daukaka kara ba
Fitacce kuma gogaggen 'dan siyasar jihar Adamawa, Malam Nuhu Ribadu, yace ya rungumi hukuncin kotun daukaka kara don haka ba zai je zuwa kotu koli ba.
Yace wannan ya biyo shawarin da yayi ne da 'yan uwa, abokan arziki, magoya baya da jiga-jigan jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng