Sunayen Wadanda Suka Mutu a Hadarin Mota Bayan Taron Tinubu a Kano Sun Fito
- Wasu magoya bayan APC sun mutu a wajen dawowa daga kamfe da Bola Tinubu ya yi a Kano
- Mutanen Kwanar Dangora su na zaman makokin rasa rayuka 7 a dalilin hadarin mota da aka yi
- Motar Volkswagen Golf da ta dauko mutane ta aukawa tankar mai, a nan mutum biyar suka cika
Kano - Mutane bakwai aka tabbatar da sun rasu a sandiyyar wani hadarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kano zuwa Zaria a ranar Larabar nan.
Daily Trust ta ce wadannan mutane su na dawowa gida daga wajen taron yakin neman zaben Bola Tinubu da APC ta shirya, sai abin ya faru.
Wadannan Bayin Allah da suka cika sun fito ne daga garin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru, sun je Kano wajen gangamin APC.
Wani wanda hadarin ya auku a gabansa, ya ce da kimanin karfe 6:00 na yamman Laraba, wata mota kirar Volkswagen Golf ta ci karo da tanka.
Yadda abin ya faru - Shaida
Mutane goma suke cikin motocin yayin da Golf din ta bugi katuwar tankan mai kafin rana ta fadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tukur Lawan wanda mazaunin Kwanar Dangora ne, ya ce nan-take mutane biyar suka mutu, yayin da sauran biyu suka mutu bayan kai su asibiti.
An bada sanarwar mutuwar ragowar fasinjojin ne a babban asibitin Murtala Muhammed na Kano.
Shi ma Tukur Lawan ya ce da shi aka halarci gangamin nan Bola Tinubu a birnin Kano, amma a kan hanya sai hadari ta rutsa da mutanen garinsu.
"Duk mun je wajen taron, a kan hanyarmu ne sai mumunan lamarin ya auku. Mun tashi yau da jimami.
Bayan sun yi karo, sai tankar ta balle daga jikin motar, ta murkushe Golf din a kan jakin Babangida a kan titi."
- Tukur Lawan
Sunayen wadanda suka rasu
Majiyar da aka zanta da ita ta bada sunayen wadanda suka riga mu gidan gaskiya da: Bala Kariya, Barau Kariya, Hamza Huntu, da Danladi Gidan Algaita,
Ragowar su ne Musbahu Gidan Diraman, Yakubu Gidan Diraman da Lawan Gidan Diraman.
Mahmud Abubakar Kiru ya fadawa jaridar cewa mutuwar ta girgiza Kiru, ya ce manyan ‘yan siyasa sun halarci sallar jana’izar da aka yi masu a jiya.
Sanata Kabiru Gaya yana cikin wadanda aka yi sallar gawa da su. Duk abin da ya faru, jami’an hukumar FRSC sun ce ba su san da labarin hadarin ba.
'Yan APC na goyon bayan Atiku?
Rahoton da aka samu dazu ya nuna Gwamnoni 11, da Sanatoci fiye da 30 a majalisar dattawa su na taimakon takarar Atiku Abubakar ta bayan fage a APC.
Daniel Bwala ya yi wannan ikirari da aka yi hira da shi, amma ya gagara fadan sunayen wadanda za su ci amanar Bola Tinubu a zaben watan Fubrairu.
Asali: Legit.ng