Tinubu Ya Sake Rasa Dama, Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP
- Tsohon kakakin majalisar jihar Kogi ya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC tare da komawa jam’iyyar adawa ta PDP
- Rahoto ya bayyana cewa, akalla mabiyansa 3000 ne suka shiga PDP tare dashi a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu
- Jam’iyyun siyasa na ci gaba ganin wani yanayi mai kama da musayar mambobi yayin da zaben 2023 ke karatowa
Lokoja, jihar Kogi - Alfa Imam, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kogi ya bayyana shiga jam’iyyar PDP tare da ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki.
A cewar rahoton Tribune Online, kakakin na majalisar dokokin jihar Kogi ya fice daga jam’iyyar ne tare da magoya bayansa da basu yi kasa da mutum 3000 ba a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu.
Imam ya jagoranci mabiyansa zuwa PDP a karamar hukumar Lokoja, inda yace jam’iyyar ta su Buhari ta gaza samar da romon dimokradiyya.
Tsohon kakakin ya kuma bayyana cewa, ya kuma yaba da tsarin PDP da yadda abubuwa ke tafiya a ciki, inda ya kara da cewa, ya jima yana zaman wahala a jam’iyyar APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dalilin da yasa tsohon kakaki ya bar APC, ya shiga PDP
Ya kuma ce, shigarsa jam’iyyar PDP ba yana nufin sauya riga ce kawai ba, ya bar APC ne tare da shiga PDP donzama mamban jam’iyya mai tsarin shugabanci nagari., Daily Post ta tattaro.
Da yake bayyanawa karara cewa APC ba ta da ingantaccen shugabanci, Imam ya ce ya zauna a jam’iyyar ne domin magance wasu kura-kurai, amma hakan ya gagara.
Ya kuma tuna yadda a baya ya yi gangamin nuna adawa da PDP a jihar, amma a yanzu ya yi dana-sanin cewa, ‘yan Najeriya sun dandana azaba a karkashin mulkin APC.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, tabbas PDP za ta ci babban zabe a 2023 kuma ya samu dama mai kyau a yanzu na shiga jirgin PDP.
Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Na Arewa Ke Son Tinubu Ya Gaji Buhari a Zaben Bana
A wani labarin, kunji yadda gwamnan Arewa ya bayyana dalilin da yasa gwamnonin Arewa na APC ke kaunar dan takarar shugaban kasa Tinubu.
Ya ce kaunar da 'yan Arewa ke yiwa Tinubu ba komai bane face don ba 'yan Kudu maso Yamma su samu damar mulki.
An ce wasu gwamnonin APC suna kokarin hada kai don tabbatar da Atiku ya zama shugaban kasa a 2023.
Asali: Legit.ng