2023: Atiku Zai Kawo Sauyi a Siyasar Najeriya, Ku Zabe Shi - Tambuwal

2023: Atiku Zai Kawo Sauyi a Siyasar Najeriya, Ku Zabe Shi - Tambuwal

  • An ba yan Najeriya tabbacin cewa abubuwa za su inganta idan Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa na gaba
  • Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ne ya bayar da tabbacin a ranar Talata, 3 ga watan Janairu
  • Tambuwal ya ce Atiku na da dabaru mafi kyawu na kawo karshen ta’addanci, yaki da rashawa da inganta ababen more rayuwa a kasar

Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, shine dan takara daya tilo da zai iya sauya makomar siyasa Najeriya zuwa mai kyau.

Tambuwal, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya yi wannan hasashen ne a wajen yakin neman zaben jam'iyyar a kananan hukumomin Binji da Tangaza da ke jihar, a ranar Talata, 3 ga watan Janairu, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Daukarwa Al'ummar Arewa Gagarumin Alkawari a Bangaren Almajiranci

Atiku da Tambuwal
2023: Atiku Zai Kawo Sauyi a Siyasar Najeriya, Ku Zabe Shi - Tambuwaln Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Atiku zai magance ta'addaci, rashawa da bunkasa tattalin arziki, Tambuwal

A cewarsa, Atiku ya tsara manufofi da za su yi aiki don kawo karshen ta'addanci, yaki da rashawa, rashin aiki, magance tabarbarewar ababen more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yan Najeriya da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tambuwal ya ce:

"Saboda haka, mu baiwa yan takarar PDP kuri'unmu tun daga shugaban kasa zuwa yan majalisar dokokin jiha domin cin gajiyar Najeriya mai inganci da muke mafarki.
"Mu tsare katunan zabenmu sannan mu guji duk mutumin da zai yi amfani da kudi wajen siye kuri'unmu don goben kasarmu."

Kada ku bari a yaudareku da kudi, Tambuwal ga masu zabe

Gwamnan ya kuma bukaci taron jama'ar da su ci gaba da kare mutuncinsu, yana mai cewa kada su bari ayi amfani da su wajen hargitsa zaman lafiya da barkewar rikici.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

Shugaban PDP a jihar, Alhaji Bello Goronyo, ya yi godiya ga mutanen yankin kan giyon bayan da suke ba jam'iyyar.

Bello ya tarbi wasu manyan mambobin sauran jam'iyyun siyasa wadanda a cewarsu sun ga dalilin komawa PDP tare da sauran mabiyansu.

Shugaban jam'iyyar ya yaba ma wannan hikima ta sabbin shiga jam'iyyar, yana mai bayyanasu a matsayin abokan nasara.

A nashi bangaren, dan takarar gwamnan PDP, Malam Sa'idu Umar, ya yi alkawarin ci gaba daga inda Tambuwal ya tsaya idan aka zabe shi, rahoton Pulse.

Zan inganta tsarin Almajiranci idan na zama shugaban kasa, Tinubu

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin inganta tsarin Almajiranci idan aka zabe shi a matsayin magajin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Tinubu ya ba da tabbacin ne yayin da yake zantawa da shugabanni da malaman Musulunci a jihar Kano a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Wanda Yake Goyon Baya Ya Gaji Buhari a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng