Hotunan Bola Tinubu Yayin da Ya Dawo Najeriya Daga Kasa mai Tsarki
- ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Abuja bayan kammala aikin Umra da yaje kasa mai tsarki
- Tinubu tare da mukarrabansa sun sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja bayan kammala Umra
- An gan shi tare da Gwamna Badaru na jihar Jigawa tare da wasu magoya bayansa inda suka sauka a daren Lahadi da ta gabata
FCT, Abuja - Bola Ahmed Tinubu, ‘Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya dawo Najeriya bayan Umra da yake yi kasar Saudi Arabia.
Tinubu ya ziyarci kasar Saudi Arabia ne don yi Umra.
A watan Afirilu, ‘dan takarar APC din ya ziyarci kasa mai tsarki kafin yayi caraf da tikitin takarar kujerar shugabancin masa ta jam’iyyar.
Tinubu wanda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Lahadi da dare, ya samu tarba ta musamman daga Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga hotunansu:
Bola Tinubu ne dai ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC wanda ya lallasa sauran ‘yan takarkarin da suka tsaya neman tikitin kamar su Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da sauransu, wadanda suka lale Naira miliyan dari suka siya fom.
Tun bayan nan, Tinubu ya tabbat halastaccen ‘dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar inda yanzu yake ta yawon kamfen din zabensu da za a yi a watan Fabrairu jiha-jiha a fadin kasar nan.
Za a iya cewa kusan dukkan ‘yan jam’iyyar APC suna bashi goyon baya dari bisa dari tare da mataimakinsa, Alhaji Kashi Shettima na jihar Borno.
Sun zagaya jihohi kamar su Kaduna inda suka ziyarci wadanda ta’addancin ‘yan bindiga ya ritsa dasu a yankunan Birnin Gwari.
Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje jama’a mazauna yankunan Birnin Gwari da matsalar rashin tsaro ta ritsa dasu N50 miliyan.
Ya kara da shan alwashin ganin bayan ta’addanci a yankin matukar yayi nasarar cin zaben shugaban kasa da za a yi a shekarar 2023 dake gabotowa.
Daga nan sarkin Birnin Gwari ya mika godiya tare da gwangwaje shi da sarautar gargajiya.
Asali: Legit.ng