Gwamnonin Da Zasu Ci Taliyar Karshe a Wannan Shekarar Yayin Da Wa'adinsu Na Biyu Ke Karewa
- Gwamnonin daga jam'iyyar PDP da APC na kare wa'adin mulkinsu a karo na biyu bayan shafe shekaru takwas.
- Ana yawan gwanin gwamnonin neman takarar sanata ko wani mukami a gwamnatin mai zuwa dan samun madafa
- Daga cikin gwamnonin akwai gwamnonin kudu da arewa, kamar Badaru Abubakar na Jigawa da takwaransa na jihar Katsina da kano harma da kaduna.
Nigeria - Gabannin babban zaben shekarar 2023, wasu daga cikin gwamnonin Nigeria na sallama ko bankwana da kujera gwamnan, sannan kuma zasu tashi ba tare da neman kowanne mukami ba
Wasu daga cikin gwamnonin sun dukafa dan ganin marawa wani dan takara ko kuma na jam'iyyarsu baya dan ganin sun sami wani mukami da za'a tafi dasu a mulkin gaba.
ga wasu gwamnonin da wa'adinsu zai kare:
Simon Bako Lalong (Plateau)
2023: Magana Ta Kare, Wike da Ortom Sun Hada Baki, Sun Yi Magana Kan Dan Takarar da G5 Zata Marawa Baya
Simon Lalong na sallama da kujerar gwamnan jihar Plateau bayan kare wa'adin mulkinsa na biyu. Lalong ya dare kan kujerar gwamnan jihar ne bayan da aka samu guguwar sauyi da akayi a kakar zaben shekarar 2015.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A karan farko kenan da jam'iyyar adawa ta mulki jihar bayan da jam'iyyar PDP ta mulketa tsahon shekara 16. A yanzu dai Lalong shine shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu
Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa)
Badaru wanda yake gwamnan jihar jigawa zai attare komatsansa daga fadar gwamnatin jihar jigawa a lokacin rantsuwar sabon gwamnan da yan jihar zasu zaba a shekarar nan.
Badaru yayi takarar gwamna a shekarar 2011 a karkashin jam'iyyar ACn inda bai samu nasara ba, sai a zaben 2015 inda ya samu nasara kan dan takarar gwamnan jihar na PDP.
Badaru dai ya rungumi tafiyar Bola AHmed Tinubu ka'in da na'in domin ganin ya samu wani wajen dafewa bayan kammala gwamnatinsa inda Tinubun yakai ga gaci
Samuel Ortom (Benue)
Ortum ya samu damar kada abokin gwarminsa a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2015, to sai dai ko talata biyar ortum din bai ci ba ya sauya sheka tare da komawa jam'iyyar PDP, kuma ya samu damar kara darewa a jam'iyyar PDP
To sai dai a lokacin da wa'adin gwamnatin Ortum din yake karewa, gwamnan ya tsunduma fada da dan takarar shugaban kasar Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, inda ya hadu da sauran yan uwansa gwamnoni tare da cewa jam'iyyar PDP batai musu adalci ba.
David Umahi (Ebonyi)
Gwamnan jihar Ebonyi yayi kaurin suna wajen ganin an bawa dan arewa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, to sai dai bayan samun takarar Bola, Umahi ya matsa kan daukar mataimaki daga arewa kuma ya kasance musulmi.
Duk da gwaman umahi na da fada aji a jiharsa, gwamnan ya matsa wajen taimakawa dan takarar APC din dan ganin samun wani matsugunni a gwamnatin APC in ta kai ga gaci
Ifeanyi Okowa (Delta)
Gwamna Ifenyi Okowa na kare wa'adin mulkinsa na biyu a jihar Delata karkashin jam'iyyar PDP.
To sai dai za'a iya cewa kaf cikin gwamnonin Nigeria masu kare wa;adinsu babu wanda ya kai Okowa dace, domin shine yake takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyarsa ta PDP.
Okowa wanda daukansa takarar ne ya janyo kirkira mo kuwa samuwar darewar wasu gwamonin jam'iyyar inda suke kiran kansu da G5.
Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)
Ifeanyi Ugwuanyi ma dai na kokarin kai batensa bayan kare wa'adin mulinsa na biyu a jihar Enugu da take a kudu maso gabashin Nigeria.
Darius Dickson Ishaku (Taraba)
Takarar Emmenuel Bachwa ta bawa gwamnan jihar taraba Ishaku damar takarar sanat yayin da Bachwa din kuma yake takarar gwamann jihar a karkashin jam'iyyar PDP.
Indai So Ake A Magance Matsalar Tsaro Da Satar Dukiyar Kasa To Atiku Ne zai Iya Magance Su, Tambuwal
Ishaku dai na karasa wa'adin mulkinsa a karo na karshe bayan darewa kan kujerar gwamnan jihar a shekarar 2015.
Aminu Tambuwal (Sokoto)
Gwamnan jihar Sokoto na kare wa'adin mulkinsa na biyu bayan da ya samu damar darewa kan karagar mulkin jihar Sokoto a karkashin jam'iyyar APC, to sai dai kuma tambuwal din ya tsinci larabarsa a talata inda yayi mi'ara koma baya ya dawo jam'iyyarsa ta PDP.
Yanzu haka Tambuwal ne shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, kuma yana takarar sanata a jihar tasa.
Sauran Gwamonin
Sauran gwamnonin da zasu yi bankwana da kujerun sun hada da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, Gwamnan JIhar Kwara Abdurazaq Abdurahman, da Gwamnan jihar Kano Dr ABdullahi Umar Ganduje.
Asali: Legit.ng