2023: Sama Yan Najeriya Miliyan Biyu Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Jihar Legas da Abuja

2023: Sama Yan Najeriya Miliyan Biyu Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Jihar Legas da Abuja

Kasa da watanni biyu gabanin babban zaben 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa akalla mutane 2,181,059 a Legas da Abuja ne zasu rasa damar kada kuri'a.

Hukumar INEC ta ce adadin wadannan mutane zasu rasa damarsu ne saboda har yanzun ba su je sun karbi katin zabe PVC ba a yankunansu.

Hukumar ta kara jaddada cewa duk da karancin zuwa karban katin zabe, ba zata lamurci wani ya turo wakili don amsar masa katin PVC ba a dukkan sassan kasar nan.

Matakan zabe a Najeriya.
2023: Sama Yan Najeriya Miliyan Biyu Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a Jihar Legas da Abuja Hoto: vanguard
Asali: Depositphotos

A wani kundin bayanai da jaridar Vanguard ta ranar Lahadi ta samu daga INEC a jihar Legas da Birnin tarayya Abuja, ya nuna cewa mutane 7,510,491 ne suka karbi katin zabe a Legas.

Haka zalika mazauna Abuja 1,075,211 sun zo sun karbi damarsu ta kada kuri'a. Amma ɗaya bangaren har yanzun katin PVC 230,007 na nan a jibge ba'a karba ba a Abuja tsakanin 2011-2019.

Kara karanta wannan

Ma’aikata Sun Bada Sharadi Kan Karin Albashi, Sun ce ba Shi Kadai Ake Bukata ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan sun kuma kara da cewa a cikin sabbin rijista 305,960 da aka yi tsakanin 2021 da 2022, har yanzun akwai ragowar 230,636 da masu su ba su je sun amsa ba.

A daya daga cikin daftarin bayanan mai taken, "Rahoton INEC na PVC a Legas," ya nuna cewa tsoffin katin zaɓen da suka isa jihar sun kai 6,570,291, zuwa 27 ga watan Disamba, an karbi 6,652,515, kati 917,776 na nan jibge.

Rahoton ya kuma nuna cewa hedkwatar INEC ta kasa ta kawo sabbin katuna 940,200 jihar Legas, mutane sun karbi 137,560 zuwa 27 ga watan Disamba, 2022, ya rage saura 802,640.

"Jimullar katin zabe da hedkwata ta aiko mana sune 7,510,491, zuwa 27 ga watan Dismba, 2022, mutane sun karbi katuna 5,790,075, ya rage saura jimulla 1,720,416."

Da yake jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki, kwamishinan zabe a jihar Legas, Mista Olusegun Agbaje, ya ce:

Kara karanta wannan

Babban aiki: 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 21, sun ceto mutum 206 daga hannunsu

"Katunan da ba'a amsa ba suna nan a Ofisoshin INEC na faɗin jiha, amma ba mu yarda wani ya karban wa wani ba kuma karban Katin zabe kyauta ne."

Wike ya maida martani ga gwamna Okowa

A wani labarin kuma Abokin Takarar Atiku Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Wike Ya Masa Zazzafan Martani

Gwamna Wike, jagoran G-5 ya maida zazzafan martani kan kalaman da Okowa ya yi cewa Allah ke ba da mulki ba gwamnonin G5 ba.

Wike, wanda ke gab da fadin dan takarar da zai wa aiki a 2023, yace sanin Allah ne ma ya sa tafiyar G5 ke kara karfi a kowace rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262