Rikicin PDP: Sabon Tashin Hankali Ya Billo Yayin da Ayu Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kan Tsagin Wike
- An tattaro cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya kaddamar da sabon hari kan tsagin Gwamna Nyesom Wike
- Hasashe sun nuna cewa Ayu ya soke jerin sunayen wakilai wanda Wike da gwamnonin G5 suka mika sakatariyar PDP na kasa
- A cewar majiyar, shugaban PDPn na kasa da tawagarsa sun yanke shawara kan abun da suka bayyana a matsayin dalili na kariya
Abuja - Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, ya kaddamar da sabon hari a kan fusatattun gwamnonin jam'iyyar wadanda aka fi sani da gwamnonin G-5
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ana iya bayyana wannan sabon mataki da Ayu ya dauka a matsayin zazzafan martani ga tsagin Gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar.
An tattaro cewa Ayu ya soke jerin sunayen wakilan zabe da gwanonin suka tattara sannan suka aika sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja.
Rawar ganin da wakilan zabe za su taka a zaben 2023
Ana sanya ran sakatariyar PDP za ta gabatar da jerin sunayen ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku lura cewa wakilan jam'iyya da INEC ta tantance su kadai za a bari su tsaya a rumfunan zabe da cibiyar tattara sakamakon zabe.
An tattaro cewa shugaban PDPn na kasa ya nuna fargaba a kan yiwuwar yarda da mika makomar jam'iyyar a hannayen wadanda gwamnonin suka zaba.
Halin da ake ciki game da PDP, zaben 2023, Iyorchia Ayu, Nyesom Wike, da gwamnonin G5
Kamar yadda yake a dokar zabe, kowace jam'iyyar siyasa za ta samu wakili a kowace rumfar zabe da cibiyar tattara sakamako a fadin kasar.
Dokar zabe ya kuma bukaci wakilan su sanya hannu a sakamakon zabe kafin jami'in zabe ya bayyana sakamakon zabe a rumfar zabe da cibiyar tattara sakamako.
A cewar majiyar, shawarar da Ayu da tawagarsa a sakatariyar PDPn suka yanke na tantance jerin sunayen wakilan na gwamnonin G5 da wasu yan jihohi ya kasance saboda dalilai na kariya.
Yan Najeriya a Turai sun yi wa Atiku alkawarin kuri'u miliyan 1
A wani labarin, wasu fitattun yan Najeriya mazauna Turai sun ce Atiku Abubakar shine ya fi cancanta ya zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.
Kungiyar ta yi alkawarin kawowa dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar PDP kuri'u miliyan daya daga bangarenta a zaben kasar mai zuwa.
Asali: Legit.ng