Gwamna Emmanuel Udom Ya Sanya Labule Da Wike, Ortom a Birnin Fatakwal

Gwamna Emmanuel Udom Ya Sanya Labule Da Wike, Ortom a Birnin Fatakwal

  • Babban gwamnan PDP kuma jagora a kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ya sanya labule da gwamna Wike
  • Gwamna Udom Emmanuel ya kai wa takwaran sa na jihar Ribas ziyara ne a karon farko tun bayan da suka sha kashi a hannun Atiku
  • Gwamnonin biyu bayan sun kammala ganawar sirri sun bayyana maƙasudin wannan ziyarar ta bazata da Udom ya kawo

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, ya gana da takwaran sa na jihar Ribas, Nyesom Wike, ranar Asabar a birnin Fatakwal.

Emmanuel da Wike, waɗanda su duka sun yi takarar neman kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen fidda gwani wanda Atiku Abubakar ya lashe, basu taɓa wata ganawa ba tun bayan wannan lokacin.

A yayin da Emmanuel yake ɗaya daga cikin shugabannin yaƙin neman zaɓen PDP na shugaban ƙasa, Wike da abokanan sa sun nesanta kan su da yaƙin neman zaɓen Atiku.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Sai dai a ranar Asabar, Emmanuel tare da rakiyar gwamna Ortom, mamba a tawagar G5, sun ziyarci Wike inda su duka ukun suka gana a sirrin ce. Rahoton Jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Gwamna Emmanuel da su Wike.
Gwamna Emmanuel Udom Ya Sanya Labule Da Wike, Ortom a Birnin Fatakwal Hoto: dailytrust
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan taron na su, Wike yace dangantakar sa da Emmanuel bata gushe ba duk kuwa da bambancin siyasa dake a tsakanin su.

Wike ya ce:

"Siyasa ba itace abinda zai raba ƴan'uwa ya raba abokai ba. Kowa ya san dangantaka ta da Udom, sannan za mu cigaba da mutunta juna. Za mu iya samun bambanci ra'ayin siyasa."
"Hakan bai kamata ya raba ƴan'uwantakar mu ko yasa muyi nesa da juna ba. A cewar gwamna Wike."

Abinda da sa na kawo wa Wike ziyara - Emmanuel

A nasa ɓangaren, Udom yace ziyarar sa bata siyasa bace, amma sai domin nuna ƙauna ta 'yan'uwantaka a dalilin wannan lokacin shagulgula.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Ya Karaya, Ya Faɗi Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Idan G-5 Suka Koma Bayan Tinubu

Tabbas wannan lokacin nuna ƙaun ne. A cikin wannan lokacin idan bamu nuna ƙauna ba, ƙaunar da ba a nuna ta bata da amfani. Ina tunanin abinda muke ƙoƙarin nunawa kenan, ƙaunar ƴan'uwantaka da abota.
Sannan domin wannan lokacin dole mu kai wa juna ziyara. A cewar sa.

An Shiryawa Atiku Abubakar Wani Gagarumin Tattaki a Katsina

Wata gamayyar ƙungiyoyin siyasa sun shiryawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP wani gagarumin tattaki a jihar Katsina.

Aƙalla sama da ƙungiyoyin siyasa 70 ne suka fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su domin tattakin nuna goyon baya ga Atiku.

A cewar shugaban shirya tattakin, sun gaji da mulkin jam'iyyar APC wanda ya kawo yunwa, talauci da rashin tsaro a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262