Mu Zamu Yi Nasara Duk Da Ƙawancen G5 da Tinubu -Gwamna Okowa
- Mataimakin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa ubangiji yana tare da su a zaɓe mai zuwa
- Gwamna Okowa na jihar Delta ya nuna cewa nasara na ga jam'iyyar PDP duk kuwa da ƙawancen da G5 za suyi da Tinubu
- Gwamnan yayi fatan cewa gwamnonin na G5 su dawo su marawa PDP baya domin ɗarewakan madafun ikon ƙasar nan a 2023
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Sanata (Dr) Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa ubangiji ne kaɗai zai samar da shugaban ƙasar Najeriya na gaba ba wai abinda gwamnonin G5 za suyi ba.
Okowa ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a Aboh lokacin da ya jagoranci yaƙin neman zaɓen PDP na jihar Delta a ƙananan hukumomin Ndokwa ta Gabas da Ndokwa ta Yamma a jihar. Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Sai dai, gwamnan ya nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa gwamnonin biyar za su manta da dukkanin abinda ya fari a baya suyi aiki tukuru wajen ganin jam'iyyar PDP tayi nasara a zaɓen 2023
Gwamna Okowa ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ubangiji yace mu ƴan PDP za mu lashe wannan zaɓen. Abubuwa da dama na faruwa yanzu sannan mutane na tambayar ya batun gwamnonin G5."
Waɗan nan gwamnonin 'yan'uwan mu ne, kowa yana da muhimmanci. Amma abinda ubangiji ya ƙaddara zai auku, ba wanda ya isa ya sauya shi.
"Don haka koda wasu daga cikin su sun zaɓi su goyawa APC baya, wasu za su tsaya tare da mu domin za a samu rabuwar kai a tsakanin su."
Duk abinda G5 zasu yi dai PDP ta karbi mulki - Okowa
A rahoton The Cable, Okowa ya ci gaba da cewa:
"Maganar gaskiya itace ina da matuƙar hangen nesa a siyasa kuma na tsaya na lura da kyau cewa duk abinda za suyi, PDP zata lashe zaɓe mai zuwa da yardar unabgiji."
"Ƙarfin ikon ubangiji ne kaɗai zai sanya mu samu nasara. Saboda haka koda ƴan G5 sun ce za su marawa APC ko wata jam'iyyar daban baya, mu ne zamu yi nasara. A cewar gwamnan."
PDP Zata Ladabtar Da Wike Lokacin Da Ya Dace -Gwamna Tambuwal
A wani labarin na daban gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana lokacin da jam'iyyar PDP zata hukunta su Wike da ƴan tawagar G5.
Gwamnan yace jam'iyyar ba zata kyale duk wani ɗanɗanta ba da ya kasance yana da ɗabi'ar saɓawa kan abinda take so.
Wannan na zuwa ne yayin da tawagar G5 karkashin gwamna Wike ke shirin bayyana ɗan takarar da zata marawa baya a 2023.
Asali: Legit.ng