Zaben Gwamnan 2023: Kotu Ta Sake Ayyana Abacha a Matsayin Dan Takarar PDP a Kano

Zaben Gwamnan 2023: Kotu Ta Sake Ayyana Abacha a Matsayin Dan Takarar PDP a Kano

  • Kotun tarayya a Jihar Kano ta sake tabbatar da halascin Mohammed Abacha a matsayin dan takarar gwamnan PDP
  • Kotun ta ayyana cewa Abacha shine halastaccen dan takarar jam'iyyar a zaben 2023 kuma ta kori karar da Jafar Bello ya shigar
  • Alkali ya ce rashin kasancewar sunan dan takarar a rijistan PDP a gudunmar Fagge bai isa ya hana shi shiga zaben fidda gwanin jam'iyyar ba

Kano - Wata babbar kotun tarayya a Kano ta yi watsi da wata kara da Jafar Bello ya shigar inda yake kalubalantar zaban Mohammed Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar.

Mista Bello, babban abokin hamayyar Abacha a zaben fidda gwanin PDP da aka yi a watan Mayu, ya nemi a soke zaben sa.

Kara karanta wannan

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Mohammed Abacha
Zaben Gwamnan 2023: Kotu Ta Sake Ayyana Abacha a Matsayin Dan Takarar PDP a Kano Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Har wayau, Bello ya yi ikirarin cewa sunan Abacha baya cikin rijistan mambobin PDP a gudunmar Fagge, karamar hukumar Fagge inda daga nan ne dan takarar ya fito saboda haka, a cewarsa bai cancanci tsayawa takarar zaben fidda gwanin ba.

Rashin sunan Abacha a rijistan Fagge bai isa hana shi takara ba, alkali

Da yake zartar da hukunci a ranar Laraba, mai shari'a Abdullahi Liman, ya riki cewa rashin sunan Abacha a rijistan PDP a Fagge bai isa ya hana shi yin takara a zaben fidda gwanin ba, Premium Times ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta riki muhawarar da lauyan Abacha, Reuben Atabo, ya yi cewa katin shaidar kasancewa dan PDP da kuma alfarmar da jam'iyyar ta yi masa sun isa su bashi damar shiga zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Alkalin ya kuma riki cewa bayan samun kuri'u mafi yawa a zaben fidda gwanin da aka yi, Mista Abacha ne ya lashe zabe kuma shine sahihin dan takarar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu ko Obi? Daga Karshe, Miyetti Allah Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Za Ta Zaba

Baya ga Abacha, Bello ya lissafa PDP, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) Sadiq Wali cikin wadanda ake kara, rahoton Independen Post.

Wannan nasara da Abacha ya sake yi na zuwa ne kimanin mako guda bayan kotun ta ayyana shi a matsalin halastaccen dan takarar gwamnan PDP a jihar Kano.

Kotu ta Kori Wali, ta tabbatar da Abacha dan takarar gwamnan PDP jihar Kano

Idan za ku tuna, Mista Wali ma ya sha kaye a hannun Abacha a babban kotun tarayya ta Kano.

Da farko, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta saki sunan Mista Wali, dan tsohon ministan harkokin waje Aminu Wali, a matsayin dan takarar gwamnan PDP.

Abacha wanda ya kasance dan tsohon shugaban kasa a mulki soja, Sani Abacha, ya kalubalanci Mista Wali a kotu kuma ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng