Sarakuna Sun Tsinewa Masu Neman Takara Tare da Gwamnan APC a Zaben 2023
- David Umahi ya ziyarci mahaifarsa ta Uburu yayin da yake yakin neman zama ‘dan majalisar dattawa
- Gwamnan Ebonyi yana takaran Sanatan kudan jihar a karkashin APC, bayan ya rasa tikitin shugaban kasa
- Sarki Charles Mkpuma ya tsinewa duk wanda bai goyon bayan takarar Sanatan da Umahi yake yi
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya ce da karfin tsiya zai karbe kujerar Sanata mai wakiltar kudancin Ebonyi a zaben 2023 mai zuwa.
Mai girma David Umahi ya ce zai je majalisar dattawa ne domin ya yi wa mutanen mazabarsa yaki. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto dazu.
A wani jawabi da hadimin Gwamnan, Chooks Okoh ya fitar, an ji David Umahi yana cewa zai taimakawa mutanensa idan har ya zama Sanatansu.
Gwamna Umahi ya yi wannan jawabi yayin da ya ziyarci mahaifarsa ta Uburu a garin Ohazora.
Zan je in yi maku yaki a Majalisa - Umahi
“Zan je in yi yaki domin walwalar mutanen Ebonyi; ayyukan yi da abubuwan more rayuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zan yi yaki domin jama'an jihar Ebonyi su samu abin yi. Za mu karbo da karfi da yaji.”
- David Umahi
Umahi ya dace da kujerar Sanata
Okoh wanda shi ne mai taimakawa Gwamnan wajen yada labarai da tsara dabaru, ya rahoto shi yana cewa ya cancanci ya wakilci mazabarsa a 2023.
Umahi yana ganin yana da kwarewa da sanin kan aikin da zai wakilci daukacin Ebonyi da kabilar Ibo a majalisar tarayya, ba mutanensa kurum ba.
Tsinuwar Sarakunan Kasar Ibo
A rahoton Daily Trust, an ji cewa Sarakunan gargajiyan da ke Ebonyi sun yi tir da duk wani wanda yake ja da takarar Sanata da David Umahi yake yi.
Sarakunan sun ce duk mai takara ko mahalukin da yake kokarin kawowa Gwamnan ciwon-kai a wajen zaben 2023, ba zai rayu zuwa kirismetin badi ba.
Mai martaba Cif Charles Mkpuma wanda shi ne shugaban duka Sarakunan kudu maso gabashin Najeriya ya furta wadannan kalamai a kauyen Uburu.
An rahoto Charles Mkpuma yana cewa tsinuwa za ta hau kan masu yi wa Umahi adawa. Mai martaban ya yabi irin kokarin da Umahi ya yi a mulkinsa.
“Mu na goyon bayanka dari isa dari, Mai girma Gwamna. Duk wanda yake adawa da mu ba zai ga kirismetin shekara mai zuwa ba.”
- Charles Mkpuma
Za a dauki mataki kan G5
An ji labari Jam’iyyar PDP na kokarin koya darasi ga Gwamnoninta;Nyesom Wike, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, Seyi Makinde da Ifeanyi Ugwuanyi.
Ganin ba su tare da Atiku Abubakar a 2023, a dokar PDP, Jam’iyya tana da wuka da nama da za ta ladabtar da duk wani wanda yake shirya zagon-kasa.
Asali: Legit.ng