Kun yi kadan: Gwamnoninta na Kus-kus da Tinubu, PDP Za Ta Dauki Tsattsauran Mataki

Kun yi kadan: Gwamnoninta na Kus-kus da Tinubu, PDP Za Ta Dauki Tsattsauran Mataki

  • Jam’iyyar PDP ba za ta bari Gwamna Nyesom Wike su kawo mata cikas a takarar shugaban kasa ba
  • Akwai yiwuwar shugabannin jam’iyya za su ladabta ‘Yan G5 da ke yakar Atiku Abubakar a PDP
  • Dokar jam’iyya ta bada damar hukunta wanda aka samu yana bata suna ko shirya makarkashiya

Abuja - Jam’iyyar PDP za ta zama ba ta da wani zabi illa tayi amfani da dokar ta wajen hukunta Nyesom Wike da sauran Gwamnoninta da su ke mata bore.

Wani rahoto na Vanguard, ya nuna babu mamaki jam’iyyar adawar ta hukunta Gwamnonin da suka kafa kungiyar G5, su na yakar takara Atiku Abubakar.

Wata majiya daga wani shugaba a PDP ya shaida cewa Wike da mutanensa sun kawowa yakin neman zaben jam’iyya matsala da babatunsu da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Sashe na 58 (1) ya bada dama a hukunta duk wani ‘dan jam’iyya da ya yi rashin kunya, wannan doka za ta iya aiki a kan gwamnonin jihohin da mabiyansu.

Abin da dokar ta ce shi ne;

“Jam’iyya ta na da ikon ladabtar da duk ‘dan jam’iyyar da ya furta ko ya aikata abin da zai bata sunan jam’iyya ko ya jawo mata kiyayya, ko ya yi zagon-kasa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Majiya

Wannan jagora na PDP da aka zanta da shi ya ce a tsari, za a kafa kwamitin bincike ne wanda zai zauna da wanda ake zargi, bayan nan sai ya yanke hukunci.

Atiku Abubakar
Yakin neman zaben Atiku Abubakar a Jos Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Kafin nan sai jam’iyya ta gargadi wanda ake zargi da wannan laifi ta hanyar fatar baki da kuma rubutu. Bayan an ja kunnen shi ne sannan a nemi ya kare kan shi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana a Kan Wa Za a Dauka Tsakanin Tinubu da Atiku a Katsina

An gagara yin sulhu a PDP

Wani babba a PDP ya ce sun yi kokarin su sasanta da bangaren Wike, amma da alama sun yi nisa don haka ba su jin kira a adawar da suke yi wa Atiku Abubakar.

A cewarsa, jam’iyya ta na da yadda za tayi maganin wadannan matsaloli da suka bijiro mata.

Punch ta rahoto uwar jam’iyya ta PDP ta na cewa ba ta san gwamnoninta sun gana da Bola Tinubu ba, ta ce a iyaka sanin ta, hutawa ya kai Gwamnonin kasar waje.

Ra'ayin Timothy Osadalor

Timothy Osadalor wanda yana cikin ‘yan majalisar NWC, ya ce jam’iyya ta na da hurumin da za ta hukunta Gwamnonin da ke yunkurin watsi da ‘dan takaransu.

Osadalor wanda shi ne mataimakin shugaban matasan PDP na kasa, ya kalubalanci ‘Yan G5 suyi wa ‘dan takaran wata jam’iyya mubaya’a, daga nan sai a hukunta su.

Hasashen zaben 2023

An ji labari cewa hasashe ya nuna za a gwabza tsakanin Jam’iyyar APC, PDP da kuma NNPP a Jihohin Arewa, amma ba a maganar Peter Obi da LP a Yankin.

Kara karanta wannan

Hukunci 11 da Alkalai Suka Yanke a 2022 da Za a Dade ba a Manta da su a Tarihi ba

A irinsu Enugu, Ebonyi, Imo, Abia da Anambra, Obi ake ba nasara, Bola Tinubu zai iya karbe duka Jihohin Yarbawa. Watakila sai zaben ya kai zuwa zagaye na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng