Atiku, Tinubu ko Obi? Daga Karshe, Miyetti Allah Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Za Ta Zaba
- Yan watanni gabanin babban zaben shekarar 2023, jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu babban tagomashi a siyasar kasar
- Hakan na zuwa ne a yayin da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta mara wa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu baya, yayin da ya juya wa Peter Obi da wasu ke tsammanin za ta zaba baya
- Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar ta ce a ranar Juma'a ne za ta sanar da Tinubu a matsayin dan takarar da ta ke goyon baya a zaben 2023 a hukumance
Miyetti Allah Kautal Hore, kungiyar makiyaya, ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben 2023.
The Sun ta rahoto cewa goyon bayan na zuwa ne bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin kungiyar makiyayan da wakilan dan takarar shugaban kasa na APC wacce aka kamalla a baya-bayan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta yi watsi da Atiku, Peter Obi, ta mara wa Tinubu baya
An kuma tattaro cewa an cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu an rattaba hannu cewa za a yi aiki tare don tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa na APC ya ci zabe ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Da aka tuntube shi, shugaban kungiyar, Alhaji Bello Bodejo, ya tabbatar da cigaban, ya kara da cewa a ranar Juma'a kungiyar za ta sanar da goyon bayanta ga Tinubu a hukumance a taronta da za a yi a Lafiya.
Miyetti Allah ta bada dalilin goyon bayan Tinubu
Ya ce:
"Muna da babban taron mutanen mu, makiyaya fulani, da za a yi a ranar Juma'a a Lafia. A wurin taron ne za mu sanar da hukumance cewa Tinubu ne zabin mu na shugaban kasa. Idan za ka iya tunawa, makonni da suka gabata mun ce za mu sanar da dan takarar shugaban kasar mu a zabe mai zuwa kuma abin da za a yi ranar Juma'a kenan.
"Mun zauna da wakilai mun tattauna sosai kan dalilan da zai sa mu goyi bayan, bangarorin biyu sun gamsu da abin da aka cimma. Mun kuma rattaba hannu, an gama komai. Zamu fitar da wasu bayanai idan bukatan hakan ya tashi."
Zaben 2023: Daliban Najeriya sun goyi bayan Tinubu, sun bayyana dalili
A wani rahoton, Sunday Asefon, shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya su goyi bayan Tinubu a zaben 2023.
Kamar yadda The Nation ta rahoto, Asefon ya yi alkawarin ne a wurin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard.
Asali: Legit.ng