Ba Saboda Nagarta Aka Zabi Jama'ar Da ke Baibaye da Buhari ba, Jigon APC

Ba Saboda Nagarta Aka Zabi Jama'ar Da ke Baibaye da Buhari ba, Jigon APC

  • Jagoran jam'iyyar APC, Kabir Faskari ya ce akwai sake game da wasu mukaman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada
  • Hakan yayi shige da batun Matthew Kukah da yayi ranar kirsimeti, inda ya ce shugaban ya bari rashawa ta zama ruwan dare a mulkinsa
  • Kabiru Faskari ya ce, akwai mutane da dama da basu cancanci mukaman da Buhari ya nada su ba, kawai dai an dorasu ne saboda sanayya

Kabir Faskari, jagoran jam'iyyar APC ya ce akwai "sake" game da wasu mukamai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada.

A wata takarda da ya fita ranar kirsimeti, Mathew Kukah, faston Majami'ar Katolika ta jihar Sakkwato, ya zargi Buhari da gazawa a shugabancinsa ga 'yan Najeriya.

Babab Buhari ne
Ba Saboda Nagarta Aka Zabi Jama'ar Da ke Baibaye da Buhari ba, Jigon APC. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

The Cable ta rahoto cewa, ya ce shugaban kasar ya bar rashawa ta zama "ruwan dare" wanda hakan ne ya karfafa makusantansa cin kararensu ba babbaka a kasar saboda an basu wuka da nama.

Kara karanta wannan

Bana son rigima: Buhari ya fadi abu 1 da zai yi bayan sauka daga mulki a 2023

Yayin martani a wani zantawa da manema labarai a Channels TV da aka haska ranar Litinin, Faskari ya ce duk da Buhari na tsayawa tsayin daka don yakar rashawa, ba tabbacin ya bi cancanta wajen nada mukarrabansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, shugaban kasar ya tafka "kuskure" inda yayi imanin mutanen da ya yarda dasu za su yi abun da ya dace, wanda wannan "dabi'ar" ce suka yi amfani da ita a matsayin dama.

"Ina matukar kyamar rashawa. Maganar gaskiya, dari bisa dari na amince rashawa haramun ce kuma ya kamata mu sanya horo mai tsanani ga rashawa.
"A 1984, Buhari shugaban kasa lokacin yana da matukar karfi kuma kai tsaye yake dubi. A yau, yafi karkata bangaren siyasa fiye da 'yan siyasan. Kuma shekarun sun ja.
"Sannan mutanen da ya dora matsayin mukarrabansa bai dora su bisa cancanta ba. Idan za a kalli lamarin nan, dukkanmu muna da ayar tambaya.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

"Duk 'yan Najeriya na da ayar tambaya, saboda ba za ka iya kauda rashawa ba tare da samun dama da kudin yin haka ba. Dole sai kana da kudi da dama."

- A cewarsa.

"Dubi gaba daya gwamnatin. Dubi matakan. Na ga wasu jerin mukamai. Wasu matakan ana dauka ne idan an tabbatar akwai wani da ake da alfarma a wurin.
"Tabbas dama akwai suka da kushe a nan da can cikin tsarin damokaradiyya - duk mutanen da ke amsawa shugaban kasa mutane ne da ya sani saboda yana da wata dabi'ar idan ya yarda da kai, a tunaninsa za ka yi komai daidai.
"Saboda haka ya tafka wannan kuskuren sannan akwai mutanen da suke nuna kamar taimaka masa suke amma kuma taimakon kansu suke. Ya kamata a zakulo wadannan mutanen a yi watsi dasu."

- Ya kara da cewa, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Da gangan na sa tafiyata ranar bazdey na, Buhari

Kara karanta wannan

A Karshe Buhari Ya Fayyace Gaskiya Game Da Batun Karin Aurensa

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace da gangan yasa dawowarsa Najeriya daga Amurka ranar cikarsa shekaru 80 a duniya.

Ya sanar da cewa ya so zama lafiya sumul ranar babu hayaniya amma wasu ma'aikatansa sai da suka hada masa karamar liyafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng