Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu
- Kungiyar Citizens Network for Peace and Development in Nigeria za ta bi Bola Tinubu a zaben 2023
- Sakataren CNPDN, Francis Okereke Wainwei ya fitar da jawabi a kan dalilinsu na goyon bayan APC
- Wainwei yana ganin babu adalci idan suka goyi bayan Atiku Abubakar daga Arewa ya dare kan mulki
Rivers - Wata shaharriyar kungiya wanda ta yi wa Goodluck Jonathan aiki a baya, CNPDN ta fara tallatawa jama’a takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
The Nation ta ce kungiyar nan za ta goyi bayan jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Kungiyar CNPDN mai kokarin wanzar da zaman lafiya da cigaba a Najeriya ta na goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya a badi.
Maganar da ake yi, tun a watan jiya kungiyar ta ayyana Asiwaju Tinubu a matsayin ‘dan takaranta, yanzu sun fara yi masa kamfe a jihohin yankin Kudu.
Gwamonin K/Kudu su sauka
CNPDN tayi kira ga Gwamnonin Kudu maso kudu su yi murabus, musamman Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa da ya zama abokin gami a jam'iyyar PDP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An rahoto Kungiyar tana zargin Gwamnonin da cin amana domin su sabawa yarjejeniyar da aka yi na cewa mulki ya koma hannun ‘Yan Kudu a 2023.
A wani jawabi da sakataren CNPDN na kasa, Francis Okereke Wainwei, ya fitar, ya ce sun amince duk za su marawa Bola Tinubu baya a zabe mai zuwa.
Wannan shi ne adalci - Francis Okereke Wainwei
Sun ta rahoto Francis Wainwei wanda mutumin Bayelsa ne yana cewa sun dauki wannan matsaya ne saboda ganin an yi adalcli, kuma an zauna lafiya.
A yanzu wannan kungiya ta soma yi wa ‘dan takaran jam’iyyar APC kamfe a garin Fatakwal da ke jihar Ribas, suka ce dole mulki ya bar hannun Arewa.
A jawabinsa, Francis Wainwei ya zargi duka Gwaanonin kudu maso kudancin Najeriya da cin amana, ya ce Nyesom Wike ne kurum wanda ya fita zakka.
Sakataren kungiyar ya yi kira ga majalisun dokokin jihohin Kudu maso kudu da su tunbuke gwamnonin yankin idan har sun ki yarda su sauka da kansu.
CNPDN ta zargi gwamnonin Neja-Deltan da karbar bashin kasonsu na 13% da ake biyan jihohi masu arzikin fetur, amma suka yi fatali da makudan kudin.
Peter Obi ko Bola Tinubu?
An ji labari Gwamna Nyesom Wike, Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom da Ifeanyi Ugwuanyi ba za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar ba.
A yanzu kan Gwamnonin na PDP zai rabu tsakanin masu cewa a goyi bayan Bola Tinubu da wadanda ke goyon bayan takarar Peter Obi a jam’iyyar LP.
Asali: Legit.ng