Gwamnonin da Suka Yi Wa Atiku Bore Sun Karkata a Kan ‘Yan Takara 2 a Zaben 2023

Gwamnonin da Suka Yi Wa Atiku Bore Sun Karkata a Kan ‘Yan Takara 2 a Zaben 2023

  • Gwamnoni 5 da suka yi fito-na-fito da Atiku Abubakar a PDP za su goyi bayan wani ‘dan takara dabam
  • Ana tunani ‘Yan G5 za su fadawa magoya bayansu su zabi Peter Obi ko Bola Tinubu ne a zabe mai zuwa
  • Da alama Olusegun Obasanjo yana goyon bayan Obi, wasu kuma sun fi ganin cin ta ga jam’iyyar APC

London - Alamu masu karfi su na nuna Gwamnonin PDP biyar da ba su goyon bayan takarar Atiku Abubakar za su bayyana matsayarsu a kan zaben 2023.

Rahoton Punch na ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022, ya nuna nan da 5 ga watan Junairun 2022, Gwamnonin jihohin za su sanar da ‘dan takaransu.

Ana tunanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo zai iya tasiri a kan zabin wadannan gwamnoni da yanzu su na taro a birnin Landan a Birtaniya.

Kara karanta wannan

An sanar da rana da wurin da Wike, gwamnonin G5 zasu sanar da dan takaran da zasu yi a 2023

Cif Olusegun Obasanjo yana da ra’ayin cewa kamata ya yi mulkin Najeriya ya koma yankin Kudu maso gabas a badi, ana zargin yana goyon bayan Peter Obi.

Obasanjo ya dage a kan LP

Watanni hudu da suka wuce, Obasanjo wanda ya mulki kasar nan tsakanin 1999 da 2007 ya zauna da wadannan Gwamnoni a Landan, ya tallata masu Obi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Peter Obi yana neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta LP. A cikin manyan ‘yan takaran 2023, shi kadai ya fito daga Kudu maso gabas.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yana kamfe a Katsina Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Hadimin wani daga cikin ‘Yan G5 ya shaidawa Punch cewa wasu daga cikin Gwamnonin nan na duba yiwuwar bin shawarar tsohon shugaban Najeriyar.

A ba Ibo mulki a 2023

Obasanjo yana ganin idan daga Kudu za a fito da shugaban kasa, kamata ya yi a je Kudu maso gabas, yankin da bai taba samun damar rike shugabanci ba.

Kara karanta wannan

Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu

Majiyar ta ce wannan shi ne abin da ya sa Obasanjo ya zauna da Gwamnonin a Landan a watan Agusta. A gefe guda ana tunanin wasu na goyon bayan APC.

A saurari 5 ga watan Junairu

Har ila yau, majiyar ta bayyana cewa zuwa mako mai zuwa sa a wadanda abokan rigiman na Atiku Abubakar za su marawa baya a zaben shugabancin kasar.

A ranar 5 ga watan Junairun shekara mai zuwa, Gwamna Seyi Makinde zai kaddamar da yakin neman tazarce, a ranar ‘Yan G5 za su fito da ‘dan takararsu.

Wasu na kusa da Gwamnonin sun bayyana cewa babu sabani a kan goyon bayan ‘Dan Kudu ya karbi mulki tun da Atiku ya ki yarda a sauke shugaban PDP.

Kwankwaso ya ragargaji Atiku, Tinubu

An rahoto Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa ya fi abokan gabansa ilmin boko, ya ce ana ta rigima a kan 'yan takaran sun yi sakandare, alhali shi yana da PhD.

Kara karanta wannan

Ni Ba Safaya Taya Bane, Ba Na Amalala: Kwankwaso Ya Yi Shagube Ga Atiku da Tinubu

‘Dan takaran Shugaban kasar a NNPP, ya ce masu takara da shi sun gaji, ba za su iya rike shugabanci ba. Kwankwaso yana nufin Bola Tinubu da Atiku Abubakar ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng