Obi ya Nada Tsohon Hadimin Obasanjo Darakta Janar na Kamfen dinsa
- Peter Obi, ya nada Akin Osuntokun, tsohon hadimin shugaban kasa Obasanjo matsayin sabon darakta janar na tawagar kamfen dinsa
- An kai ga wannan matsayar ne bayan taron da masu ruwa da tsakin jam'iyyar karkashin jagorancin Abure suka gabatar a Abuja
- Osuntokun a cewar Abure zai dasa daga inda Okupe wanda kotu ta kama da laifin wanke kudin sata, ya tsaya
'Dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya sanar a ranar Talata nadin Akin Osuntokun, tsohon hadimin Shugaba Olusegun Obasanjo, matsayin Darakta Janar na kungiyar kamfen dinsa, jaridar Punch ta rahoto.
Osuntokun ya maye gurbin tsohon DG na tawagar kamfen din Obi da Datti, Doyin Okupe, wanda ya sanar da murabus dinsa a wata wasika da ya fitar ranar Talata da ta gabata bayan babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta kama shi da laifin wanke kudin sata.
Wasikar an aike ta ne ga shugaban 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Labour Party.
Jaridar Punch ta tsakuro daga mai kula da lamurran yada labarai na Obi, Emeka Obasi, yana cewa za a sanar da nadin sabon mai jagorancin tawagar kamfen din a cikin sa'o'i 48.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma bayan wani taron tsari na jam'iyyar wanda ya samu halartar Obi, mambobin kwamitin ayyuka da wasu manyan 'yan takarar jam'iyyar da shugaban jam'iyyar na kasa, Julius Abure, an sanar da Osuntokun matsayon sabon DG kamfen din.
The Cable ta rahoto cewa, Abure ya kwatanta tsohon manajan daraktan Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyan matsayin wanda ya dace kuma mai gaskiya da ya maye gurbin Okupe.
Osuntokun ya sama shugaban jam;iyyar na yankin Kudu maso yamma bayan ya bar jam'iyyar PDP inda ya koma LP a shekarar 2022.
Okupe yayi murabus daga DG din Peter Obi
A wani labari na daban, Doyin Okupe, ya yi murabus daga matsayinsa na darakta janar na tawagar kamfen din Peter Obi da Datti Baba Ahmed.
Ya sanar da hakan ne bayan da kotun tarayya ta kama shi da laifin wanke kudin sata tare da aika shi gidan yari na shekaru 2 ko tarar N500,000 kan kowanne laifi daya cikin 26 da aka kama shi dasu.
Asali: Legit.ng