Ayarin Motocin Sanata Sun Yi Ajalin Wasu Ma’aurata a Akwa Ibom

Ayarin Motocin Sanata Sun Yi Ajalin Wasu Ma’aurata a Akwa Ibom

  • Fusatattun matasa a jihar Akwa Ibom sun gudanar da zanga-zanga a kan kisan wasu ma'aurata biyu
  • Ayarin motocin sanata mai wakiltan Eket, Misis Akon Iyakenyi, sun yi ajalin ma'aurata a hanyarsu ta dawowa daga wajen kamfen
  • An zargi Sanata Iyakenyi wacce ke neman takarar mataimakiyar gwamnan jihar Akwa Ibom a PDP da nuna halin ko'inkula kan yara uku da mamatan suka bari

Fusatattun matasa a garin Akon-Itam da ke karamar hukumar Itu ta jihar Akwa Ibom sun gudanar da zanga-zanga a kan kisan wasu ma'aurata a hanyar babban titin Calabar-Itu.

Ayarin motocin sanata mai wakiltan Eket, Misis Akon Iyakenyi, ne suka yi ajalin ma'auratan a hanyarsu ta dawowa daga Uyo, babban birnin jihar inda suka je rangadin kamfen dinta, The Nation ta rahoto.

Sanata Akon Iyakenyi
Ayarin Motocin Sanata Sun Yi Ajalin Wasu Ma’aurata a Akwa Ibom Hoto: Leadership
Asali: UGC

Sanata Iyakenyi ita ce yar takarar mataimakin gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, inda za su jera da Fasto Emo Eno, wanda ke rike da tutar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

Abun da ya fusata jama'a

Da yake zantawa da manema labarai, daya daga cikin fusatattun matasan, Kwamrad Utibe Inyang, ya yi bayanin cewa ayarin motocin sun yi ram da ma'auratan a kan babur, yayin da suke kokarin kutsa kai babban titin da ke sada jihar da Calabar, jihar Cross River.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewar abun da ya kara fusata mutanen shine rikon sakainar kashin da aka yiwa diyyar naira miliyan 2 da sanatar ta baiwa iyalin.

Ya ce:

"Miji da matan da ayarin motocinta suka kashe sun mutu sun bar kananan yara uku, don haka radadin da muke ji har yanzu shine saboda halin ko'inkula da yar takarar mataimakiyar gwamnnan ta nuna ba tare da la'akari da yadda wadannan marayun yara za su taso ba da kuma girma ba tare da iyayensu ba."

Hukumar FRSC da na yan sanda sun yi martani

Kara karanta wannan

Shahararren Dillalin Makamai, Bilyaminu Saidu, ya Shiga Hannun 'Yan Sanda a Zaria

An tattaro cewa fusatattun matasan sun jiwa wasu jami'an kula da hana afkuwar hatsarurruka da ke wajen ciwo sannan sun faffasa masu motocinsu.

Sai dai Kwamandan FRSC a jihar, Mathew Olonisaye, ya bayyana cewa motocinsu kwai aka farfasa yana mai cewa an yi nasarar daidaita lamarin.

Da yake tabbatar da lamarin, kwamishinan yan sandan jihar, Mista Olatoye Durosinmi, ya ce an dawo da zaman lafiya yankin bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, rahoton Leadership.

Ya kuma ce ba don sun gaggauta shiga lamarin ba, matasan na gab da kona wasu motocin yar majalisar.

Dan sanda ya kashe lauya a ranar kirsimeti

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani jami'in dan sanda mai mukamin ASP ya bindige wata lauya a hanyarsu ta dawowa daga coci a ranar bikin kirsimeti tare da iyalinta a yankin Ajah da ke jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel