Idan Ya Sha Tafiya Tunaninsa Zai Saitu: Matashi Ya Horar Da Mahaifinsa Saboda Ya Ki Goyon Bayan Peter Obi
- Magoya bayan Peter Obi na aiki tukuru don ganin dan takarar shugaban kasar na Labour Party ya lashe zabe
- Wani mai amfani da Twitter @daddykukiss ya ce ya daina siyawa mahaifinsa man mota saboda ya ki goyon bayan Obi
- Mai amfani da Tuwitan ya kara da cewar ya daina ba mahaifinsa damar shiga motarsa kuma cewa tafiya da kafa a wannan sanyin zai saita tunaninsa
Wani dan Najeriya mai amfani da Twitter, HAUSA MAFIA (@daddykukiss) ya dauki tsattsauran mataki a kan mahaifinsa bayan ya ki goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, gabannin babban zaben 2023.
Mutumin ya je shafin Twitter don sanar da cewar ya daina siyawa mahaifinsa man mota sannan ya hana shi shiga masa tasa motar.
Ya ce mahaifinsa ya tsaya tsayin daka kan goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, duk da lallashinsa da yake don ya marawa Obi baya.
Ya rubuta a Twitter:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina ta kokarin shawo kan mahaifina don ya zabi @PeterObi amma ya tsaya kan bakarsa sai Atiku tsawon mako guda kenan Na daina siya mashi mai sannan na hana shi shiga mota ta, yawo a kafa da wannan sanyin zai saita tunaninsa."
Yan Najeriya sun yi martani
@Beeg_Daddee ya rubuta:
"A'a, a'a, a'a! Babu dan siyasar da ya cancanci shiga tsakanin mahaifinka da kai. Dan Allah, imma Obi, Atiki ko Tinubu kawai ka zamo dan kirki ga baba.
"Kada ka kore albarkarka daga gareka. Shikenan!"
Cere, @ChrisCyere ya ce:
"Gaskiya dan kirki ne tunda ya taimakawa mahaifinsa ya yi tunani da kyau saboda idan mahaifinsa yayi kuskure kuma mutumin da bai kamata ba ya yi nasara, abubuwa za su tabarbare, kuma matsaloli da nauyin da ke kan matashin zai karu."
Homi Deus, @La_J0lz, ya ce:
"Wato soyayyarka ga danginka ya danganta da wani dan siyasa na nisa? Kai."
Diyaolu Moshood Abiola, @diyamosab1 ya ce:
"Ka tuna kaima za ka tsinci kanka a matsayin shi wata rana. Mahaufinka na hango abun da kai ba za ka iya gani ba koda ka hau dala da gwauron dutse.
"Kada ka yi amfani da shi a matsayin makamin siyasarka. Obi baya cikin tseren. Obi ba zai iya cin zabe ba. Tseren tsakanin Atiku da Tinubu ne. Ka yiwa mahaifinka alkhairi don gobenka."
Babban fasto ya fadi yadda zaben 2023 za ta kasance
A wani labarin, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen abun da zai faru idan daya daga cikin manyan yan takarar shugaban kasa ya lashe zaben 2023.
Fasto ya ce idan Atiku Abubakar ya ci zabe tattalin arzikin Najeriya zai habbaka, idan Bola Tinubu ya ci zabe Najeriya za ta inganta kadan amma idan Peter Obi ya yi nasara, talakawa za su ji dadi yayin da masu kudi za su koka.
Asali: Legit.ng