2023: 'Yan Takarar Majalisar Tarayya Na NNPP Sun Sauya Sheka Zuwa APC
- Yan takarar kujarun majalisar tarayya a inuwar NNPP a jihar Zamfara sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
- Tsohon gwamna, Alhaji Abdul'azizi Yari ne ya karbe su hannu bibbiyu tare da wasu jiga-jigai da dubbannin mambobi
- Jam'iyyar APC na ci gaba da kara karfi a Zamfara yayin da gwamna Bello Matawalle ke neman tazarce
Zamfara - Ɗan takarar Sanatan Zamfara ta arewa a inuwar jam'iyyar NNPP, Ibrahim Shinkafi, da ɗan takarar mamban majalisar wakilai a mazaɓar Shinkafi/Zurmi, Suleiman Garba, sun sauya sheka zuwa APC.
Jaridar the Cable ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'Aziz Yari ne ya yi wa Shinkafi da Garba maraba zuwa cikin inuwar APC mai mulki ranar Talatan Mafara ranar Litinin.
Ba ya ga waɗannan biyu, a cewar wata sanarwa da hadimin Abdul'aziz Yari watau Ɗahiru Marafa, ya fitar yace akwai wasu shugabannin NNPP da PDP da suka rungumi APC.
Ma'ajiyin jam'iyyar NNPP ta jiha, Suleiman Galadi da Aminu Kanoma, kodinetan wata ƙungiyar magoya bayan PDP, na cikin wadansa aka yi wa wankan tsarki zuwa APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwan ta ce:
"Shugabannin jam'iyyar NNPP a kananan hukumomin Kauran Namoda Da Zurmi na cikin masu sauya shekar. Daga cikin masu shiga APC har da Kodinetan cika burin ɗan takarar gwamna a 2023, Aminu Kanoma."
"Sakatare da kuma ma'ajiyar kungiyar, Aminu Saminu da Hajiya Ummulkhairi Aminu duk suna cikin masu tururuwar shiga APC."
A ruwayar hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN), Yari ya samu wakilcin, Tukur Danfulani, shugaban tawagar tuntuba da tattara kananan kwamitoci na kwamitin kamfe.
Yari ya yaba wa dubbanin masu sauya shekar bisa kwarin guiwar da suka nuna wajen shiga APC kuma ya basu tabbacin za'a kula da su.
Meyasa suka zabi shiga APC?
Da yake jawabi a madadin masu sauya sheka, Shinkafi yace sun yanke shawarin shiga APC ne saboda suna da yakini da imani da shugabancin Yari.
A wani labarin kuma Sheikh Ahmad Gumi yace a halin yanzun ba'a bukatar shugaban da zai murkushe 'yan bindiga
Shahararren Malamin wanda ya yi kaurin suna wajen jawo cece-kuce yace yan arewa na bukatar wanda zai yi sulhu ne da yan fashin daji.
Asali: Legit.ng